An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja
Da alama an kashe ta ne a wani wuri sannan aka kawo aka jefar da gawarta a nan.
Kangon da aka tsinci gawar matar a Abuja
An tsinci gawar wata mata da ba a iya tantance ko wace ce ba, wadda aka yankewa kai, a cikin wani kango da ke unguwar Futuna Fulani Extension da ke Bwari a birnin tarayya Abuja, da yammacin ranar Asabar.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa wannan ne karo na farko da suka taɓa fuskantar irin wannan lamari mai tayar da hankali a unguwar, inda wari da ya fara tashi a wajen ya jawo hankalin jama’a.
- Qatar ta samu makinta na farko a tarihin gasar Kofin Duniya
- Yau Lahadi za mu sanya hannu a yarjejeniya da Iran — Trump
Ya ce, “Da muka bi sawu ne muka gano gawar a cikin kangon, nan take muka sanar da jami’an ’yan sanda.”
Wani mazaunin unguwar kuma ya bayyana cewa akwai alamun an kashe matar ce a wani wuri sannan aka kawo aka jefar da gawarta a wajen.
“Da alama an kashe ta ne a wani wuri sannan aka kawo aka jefar da gawarta a nan. An ɗaure ƙafafuwanta da igiya, kuma akwai raunuka a ƙafafunta, wanda ke nuna ta yi ƙoƙarin kuɓuta kafin a hallaka ta.
“Wannan abu ya ƙara tayar mana da hankali sosai, domin muna ganin yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a yankin. Muna cikin fargaba matuƙa.”
“Muna kira ga jami’an tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari domin ceto mu daga wannan hali,” in ji shi.
Shi ma wani mazaunin yankin, Ibrahim Dogo, ya ce an gano wani bargo mai ɗauke da jini a kusa da wajen, lamarin da ke ƙara nuna cewa an iya yin kisan ne a wajen kafin a watsar da gawar a cikin kangon.
Ya ce, “Mai yiwuwa an yaudare ta aka kawo ta nan, sannan aka yi mata wannan mummunan kisa.”
Rahotanni sun ce jami’an ’yan sanda daga yankin Bwari sun garzaya wurin inda suka ɗauke gawar zuwa Babban Asibitin Bwari domin gudanar da bincike.
Wata majiya daga rundunar ’yan sanda ta tabbatar cewa an fara bincike domin gano waɗanda ke da hannu a kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu.