An tsinci gawar wata ’yar jarida a Zariya
A shekaranjiya Laraba ne mutanen da ke Gadar Sama a Kwangila Zariya a kan hanyar Kano, suka tsinci gawar wata ’yar jarida mai suna A’isha Hassan da take aiki da jaridar Mahangar Arewa dak e Kano kwance a gefan titi. Aminiya ta garzaya wurin da abin ya faru inda ta tarar da jama’a suna ta […]
A shekaranjiya Laraba ne mutanen da ke Gadar Sama a Kwangila Zariya a kan hanyar Kano, suka tsinci gawar wata ’yar jarida mai suna A’isha Hassan da take aiki da jaridar Mahangar Arewa dak e Kano kwance a gefan titi. Aminiya ta garzaya wurin da abin ya faru inda ta tarar da jama’a suna ta juyayi ganin irin yadda suka ga gawar. Wadanda Aminiya ta tattauna da su sun ce ba su san yadda abin ya faru ba, kuma ra’ayinsu ya sha bamban domin wasu cewa suke ko makasa ne suka kashe ta suka yar da gawar, wasu kuma na cewa irin direbobin nan ne ’yan wan cans suka kashe ta. Sai dai kuma sun ce idan irin su ne, to ai su shake mutum suke yi da kebur, ita kuwa wannan gawar an sare ta ne a kai har ma idon ta ya bulluko kuma sun sare ta a kafa har ta karye. Saboda haka wasu suna tunanin ’yan ina da kisa ne suka kashe ta. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an sanar da ’yan sanda, inda suka zo suka dauki gawar tare da jakarta suka tafi da ita. A hedikwatar ’yan sanda ta Zariya Aminiya ta tarar da ’yan sanda suna gudanar da bincike inda suka shaida mata cewa sun samu katin shaidar aikinta, kuma sun samu wayarta ta hannu a cikin jakarta inda suka tuntubi mahaifiyarta kuma yanzu haka suna kan bincike. Amma ba za su kara wani abu a kan haka ba, sai bayan kammala binciken su. Tuni aka aika gawar A’isha Hassan dakin aje gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.