An tsinci gawar ’yar shekara biyu da aka yi wa fyade
A ranar Alhamis da ta gabata ce aka tsinci gawar wata yarinya mai suna Zainab, ’yar kimanin shekara biyu da watanni uku, a layin Shika da ke Tudun Wada Kaduna. An yi zargin cewa ta mutu ne bayan an yi mata fyade. Aminiya ta tuntubi mahaifin yarinyar, Malam Hussaini Salihu Abdullahi kuma ya tabbatar da […]
A ranar Alhamis da ta gabata ce aka tsinci gawar wata yarinya mai suna Zainab, ’yar kimanin shekara biyu da watanni uku, a layin Shika da ke Tudun Wada Kaduna. An yi zargin cewa ta mutu ne bayan an yi mata fyade.
Aminiya ta tuntubi mahaifin yarinyar, Malam Hussaini Salihu Abdullahi kuma ya tabbatar da wannan labari.
“Da misalin karfe 10 na safen ranar Alhamis din makon jiya ne bayan an yi wa Zainab wanka kuma ta fita waje don yin wasa da sa’o’inta, sai muka neme ta kasa da sama muka rasa. Nan muka bazama don nemo inda take amma ba mu gano ta ba. Can bayan kamar sa’a daya ne sai muka samu labarin an tsince ta a wani filin da ba kowa a yashe, an daure mata hannuwa da kafafuwa sannan ga alamar an rarake mata dubura, al’amarin da ya sa muke tsammanin wani mara imani da tausayi ne ya yi mata fyade ta dubura kuma har ya halaka ta.” Inji mahaifin.
Ya ci gaba da cewa sun sanar da ’yan sanda kuma suka zo suka dauki gawar zuwa ofishinsu don gudanar da bincike amma daga baya suka karbo ta kuma aka yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin ’yan sanda na yankin Tudun Wada a kan batun, al’amarin ya ci tura. Sai dai kafin hada wannan rahoto wakilinmu ya samu labarin an kama wani dan kimanin shekara 48 mai suna Ahmed, inda ake zarginsa da laifin kashe Zainab.
Jim kadan da samun wannan labari ne sai wasu matasan unguwar suka bazama ofishin ’yan sanda na yankin Tudun Wada inda suka nemi a ba su wanda ake zargin don su yi masa hukunci amma abin ya faskara.
Wata majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa tuni aka iza keyar wanda ake zargin zuwa sashen gudanar da bincike na Hedkwatar Hukumar ’Yan sandan Jihar Kaduna don ci gaba da bincikarsa.