An tsinci gawar ‘yar shekara shida an yi mata fyade a masallaci

An gano gawar wata yarinya ‘yar shekara 6 da aka yi wa fyade a cikin masallacin a unguwar Kurmin Mashi da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Jihar Kaduna. Ana zargin an yi wa yarinyar fyade ne har ta mutu a cikin masallacin da ake kira masallacin gidan Malam Isa, a ranar Juma’a, 26 ga […]

An tsinci gawar ‘yar shekara shida an yi mata fyade a masallaci

Taron Jama’a a kofar gidansu yarinyar da aka kashe bayan isowar kungiyoyin kare hakkin mata da yara

An gano gawar wata yarinya ‘yar shekara 6 da aka yi wa fyade a cikin masallacin a unguwar Kurmin Mashi da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Jihar Kaduna.

Ana zargin an yi wa yarinyar fyade ne har ta mutu a cikin masallacin da ake kira masallacin gidan Malam Isa, a ranar Juma’a, 26 ga watan Yuni.

Al’ummar ‘yankin ne suka tsinci gawar ba tare da wani alamar rauni a jikinta ba, amma daga baya mai wankin gawarta ta gano cewa fyade aka yi mata.

Bayan ‘yan unguwar su tsinci gawarta ne suka kira ‘yan jarida domin a nemi iyayenta, kafin wani mutum da ya bayyana a masallacin, bayan ya duba ta, ya ce ‘yarsa ce, tun misalin karfe 10 na safe suke neman ta ba su gan ta ba.

Harabar Masallacin Malam Isa inda aka gano gawar yarinyar

Ana cikin haka ne Mai garin,  Sarkin Sabon Layi,  Alhaji Rabo Abdullahi ya sanar da ‘yan sanda suka zo suka nemi bincikar lamarin, amma mahaifin yarinyar ya ce ba ya bukatar dogon bincike, a ba shi ita ya binne ta, ya rungumi kaddara.

“Yarinyar ‘yata ce,  da safen nan ne misalin karfe 10 zuwa 11 ana min aikin rufin kwano a sama sai muka neme ta muka rasa, sai yanzu da muka ga gawarta.

“Lafiya lau ta fita, ko ciwon kai ba ta yi ba, wannan abun dai Allah ne kadai Ya sani, domin ba za mu iya gane abin da ya faru ba.

“Ba zan iya zargin kowa ba, domin wannan abu yanzu ya faru, idan wasu ne suka yi Allah Ya bayyana su, in kuma Allah ne Ya kawo mata ajali, to Allah Ya jikan ta”, inji mahaifin yarinyar.

 

‘An shafa wa gawar wani abu a fuska’

Limamin masallacin da aka tsinci yarinyar, Malam Ishaq Aliyu Umar, ya ce da misalin karfe 2:30 yana dawowa daga masallacin Juma’a sai aka kira shi a waya amma bai sami damar dauka ba, daga nan aka tura masa sakon kar-ta-kwana.

“Da na karanta sakon na ga ana fada mini cewa an tsinci gawar yarinya a masallaci ta karamar kofa, sai na yi gaggawa, muna tare da wani aminina, da muka zo gida muka duba na ga gawarta, sai ban taba ba.

“Nan take na daga waya na kira sankiranmu, da ya zo ya taho da dan jarida suka kuma kira hukuma aka yi abin da za a yi.

“Ana bincike ne wata tsohuwa ta zo ta ce ta ji ana neman wata yarinya a wani gida, ko da ta je ta fada musu sai suka zo, da suka gan ta suka ce ‘yarsu ce.

“Mu ko da muka zo muka ga gawar yarinyar mun haska da fitila saboda akwai duhu, sai muka ga fuskarta kamar an shafa mata man wanke baki ne ko wani abu, amma ba mu taba ta ba, muka daga waya muka kira sankira”, inji limamin masallacin.

Limamin Masallacin da aka gano gawar yarinyar, Malam Ishaq Aliyu Umar

 

Yadda aka gano an yi mata fyade

Aminiya ta gano cewa a wajen yi wa yarinyar wankan gawa ne aka gano cewa an yi mata fyade ne, kamar yadda matar da ta wanke ta ta shaida.

Ta ce, “Gaskiya a lokacin da muka yi wa gawar yarinyar wanka ba mu da tabbacin ko an yi mata fyade ne, amma da muka gama wankan sai muka dauko fitila muka haska sai muka tabbatar an riga an bata ta.

“Sun riga sun bata ta sossai, ko da rayuwarta ma sun riga sun tarwatsa mata rayuwa”, inji dattijiwar da tayi wa gawar yarinyar wanka.

Matar da ta yi wa gawar yarinyar wanka.

 

Allambaran! Sai an yi bincike

Ana cikin haka ne har an yi wa yarinyar sutura an sanya mata likkafani za a yi mata sallah, sai kungiyoyin kare hakkin mata da yara suka ce atafau, ba za a binne ta ba, har sai an yi bincike irin na likita, an gano musababbin mutuwarta, a kuma bi mata hakkinta, inda suka fara zuwa gidan mai garin Sarkin Sabon Layi Alhaji Rabo Abdullahi.

Hakan ya tilasta fito da gawar yarinyar daga linkafani, lamarin da ya sanya hankalin jama’ar da suka taru domin su sallace ta ya tashi, kafin daga baya Sarkin ya yi musu bayani.

“Ba ni ba, wadanda suka yi mata wanka sun tabbatar da cewa fyade aka mata, kuma sa’a hudu ke nan da rasuwar yarinyar amma wurin bai rufe ba, ko yanzu ka shiga za ka gani.

“Don haka ‘yan uwa Musulmi ina so na ja hankalinmu a kan wannan lamari, bayan addu’a mu ci gaba da addu’a Allah ya kiyaye mu.

“Sannan mu ci gaba da bai wa hukuma da masu bincike goyon baya domin a gano wadannan miyagun mutane da suke cikinmu domin a yi maganin su.

“Akwai kungiyoyi da suka bada kansu domin tabbatar da an gano wadannan miyagun mutane, don Allah duk sadda suka zo za su yi aikinsu a ba su goyon baya.

“Maganar jana’iza kuma, insha Allahu za a je asibiti da ita ne yanzu domin a karbo sakamakon bincike likitoci, don haka maganar jana’iza kuma sai gobe domin za a dawo da gawar ta ne da daddare.

“Kuma Allah Ya jikanta Ya mata rahama, shi kuma wanda ya yi wannan abu Allah Ya tona masa asiri”, inji Mai Gari Rabo Abdullahi.

Sarkin Sabon Layi, Alhaji Rabo Abdullahi

 

Ya kamata iyaye su kara kiyayewa

A nata bangaren Farfesa Hauwa’u Yusuf ta Jami’ar Jihar Kaduna, daya daga cikin wadanda suka yi tsayin daka don ganin an gudanar da bincike kafin a binne yarinyar, ta yi jawabin wayar wa iyaye mata kai a kan lamarin.

“Wannan matsalace da ta game duniya ba Najeriya kadai ba, sai dai ta fi karfi a nan Arewa. Mu mata iyaye a nan muna da sakaci, yarinya sai ta fita ta yi minti biyar a waje ba ki neme ta ba, ba ki san inda ta tafi ba.

“Wani lokacin ma iyaye ne za su ce yara su fita waje su yi wasa, don haka saboda Allah saboda Ma’aiki, domin irin wannan rana ta yau wallahi ku bar ‘yayan ku a cikin daki.

“Ku bar ‘ya’yanku a cikin gida, duk ta’adin da za su yi maku a cikin gida ya fi irin wannan abu, saboda haka ku kula.

“Kuma idan abu ya faru irin wannan ku daina rufe baki, abu zai faru da yarinya irin wannan tazo gida ki wanke ta kuma ba za ki yi magana ba, sai wanda yake mata ya ji dadi ya ci gaba.

Farfesa Hauwa Yusuf, Mai fafutukar kare hakkin mata da yara

 

A rika kai rahoton fyade da wuri, a bayar da hadin kai

“Don Allah, don Ma’aiki, ku taimaka wa iyayen gari da mu kungiyoyi masu nema muku hakki idan wannan abu ya faru ku fada da wuri, domin da an yi magana nan da wuri tun lokacin da aka gano ta da tuni anyi bincike an mata sutura an binne ta.

“Musulunci bai hana mutum ya bi hakkinsa ba. Musulunci bai hana a yi bincike ba, don haka a daina dora wa Allah abin da mutum ne ya jawo ma kansa. Mun yi tawakkali ga Allah, Allah Yaa nufa yarinyar nan ba za ta kwana yau ba, ko an yi mata fyade ko ba a mata ba, kuma ko mai akwai sanadiyyar shi.

“Amma ya kamata mu yi hattara, ku kuma iyaye maza in wannan abu ya faru ku daina cewa uwar yarinyar kul kada tayi magana.

“Yanzu da ba don mun sami uban gari da ya goya mana baya ba, da sai a je a binne yarinya a ce ba fyade ba ne, wanda ya aikata kuma ya ji dadi gobe ma ya kama ‘yar wata ya yi mata haka”, inji Farfesa Hauwa, mai rajin kare hakkin mata da yara.

 

‘Yan sanda na gudanar da bincike

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba a kai ga kame wani da ake zargi ba, amma rundunar na ci gaba da bincike.

Tuni dai aka garzaya da yarinyar babban asibitin koyarwa na  Barau Dukko da ke Kaduna inda aka gudanar da bincike kafin daga bisani aka bai wa iyayenta gawarta suka yi mata sutura.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara