An tsinci gawar ’yar shekara uku bayan janye jinin jikinta a Sakkwato
Ranar Talata da ta gabata ne al’ummar Unguwar Hungumawa da ke karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa a Jihar Sakkwato suka wayi gari da gawar wata yarinya ’yar shekara uku da ake kira Nabila Abdullahi, ba tare da sun san wadanda suka jefar da ita ba, sai dai daga baya mahaifin yariyar da ke Unguwar Madakar […]

Ranar Talata da ta gabata ne al’ummar Unguwar Hungumawa da ke karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa a Jihar Sakkwato suka wayi gari da gawar wata yarinya ’yar shekara uku da ake kira Nabila Abdullahi, ba tare da sun san wadanda suka jefar da ita ba, sai dai daga baya mahaifin yariyar da ke Unguwar Madakar Tabba ya zo da ’yan uwansa sun dauki yarinyar.
Wakilin Aminiya ya tattauna da mahaifin yarinyar lokacin da yake karbar gaisuwar rashin ’yarsa a ranar Alhamis da ta gabata, inda ya ce a ranar Talata da misalin karfe tara na dare wata mace ta dauke ’yarsa ta bi bayan gidansa ta tafi, “Ni ba na gida lokacin faruwar lamarin wadanda suka gan ta ba su zaci sace yarinyar ta yi ba, sai da sauran ’ya’yana suka zo kwanciya babu Nabila suka tambaya, inda hakan ya ankarar da ni da mahaifiyarta da ta je unguwa a lokacin faruwar lamarin,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa “Daga nan ne muka shiga bincike har muka bayar da sanarwa a masallatai da hukumomin tsaro, wayewar Laraba wani makwabcinmu ya gaya mana labarin an tsinci gawar wata yarinya a cikin wani karamin rami a Unguwar Hungumawa mu je mu bincika, muka je gidan Hakimin Unguwar don can aka kai gawar bayan an tsince ta, da na gan ta sai na koma gida don shaida wa ’yan uwa da abokan arziki abin da ya faru, daga nan muka dauko ta bayan shaida wa jami’an tsaro da hakimin ya yi saboda gudanar da bincike, kafin bisine ta kamar yadda addini ya tanada. Mun je asibbiti don sanin dalilin mutuwar, ashe jinin jikinta ne aka janye, da idona na ga inda aka huda a hannunta aka janye jininta, dubi wannan rashin imani a janye jinin yarinya ’yar shekara uku don wata manufa daban. Ba wani mataki da muke shirin dauka duk wanda ya yi wa ’yata haka na bar shi da Allah ko hukuma ma na gaya wa haka, sai dai kawai sun ce za su yi bincike kamar yadda doka ta tanada,” inji shi.
Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato ASP Almustafa Sani ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce suna nan suna bincike.