An tsinci jariri a kwali, a Zariya

A ranar Asabar da ta gabata da dare, mutanen Sabuwar Anguwa Magume suka tsinci wani jariri da aka yar cikin kwali.Kamar yadda Malam Usman Tsoho, wanda aka yar da jaririn a kofar gidansa ya shaida wa Aminiya, ya ce: “Bayan na dawo daga Sallah, misalin karfe 8:30 na dare na shiga gida ke nan sai […]

An tsinci jariri a kwali, a Zariya
An tsinci jariri a kwali, a Zariya

A ranar Asabar da ta gabata da dare, mutanen Sabuwar Anguwa Magume suka tsinci wani jariri da aka yar cikin kwali.
Kamar yadda Malam Usman Tsoho, wanda aka yar da jaririn a kofar gidansa ya shaida wa Aminiya, ya ce: “Bayan na dawo daga Sallah, misalin karfe 8:30 na dare na shiga gida ke nan sai makwabcina Malam danjuma ya yi mini sallama ya ce in fito ga wani abun mamaki a kofar gidanna. Koda na fito sai kawai na ga jariri akwali, an tsaftace shi da kayansa.”
Aminiya ta gana da mai unguwar Magume, Malam Abubakar, wanda ya tabbatar da tsintar jaririn. “Lallai an tsinci wannan jariri kuma mun fara daukar mataki domin yanzu haka an ce mu je da shi gobe Laraba ana son ganinmu gaba daya kuma ni ma ina ta iya kokarina, na kula da shi.” Inji shi.
Ya zuwa rubuta labarin nan, jaririn dai yana cikin koshin lafiya kuma an rada masa suna Abdullahi.