An tsinci jaririya an jefar da ita a Yobe

Kakakin ’yan sandan jihar ta Yobe, SP Dungus Abdulkareem ya bayyana cewa jaririyar da aka jefar ba ta wuce kwana guda da haifuwa ba.

An tsinci jaririya an jefar da ita a Yobe

’Yan sandan sun ceto wata jaririya sabuwar haihuwa da aka jefar da ita a kauyen Kalallawa da ke Karamar Hukumar Damaturu.

Kakakin ’yan sandan jihar ta Yobe, SP Dungus Abdulkareem ya bayyana cewa jaririyar da aka jefar ba ta wuce kwana guda da haifuwa ba.

Ya bayyana wa manema labarai a garin Damaturu cewar a ranar 25 ga Mayu, 2026, da misalin qarfe 15:00 na safe, jami’ansu da ke aiki a ofishin A Division a Damaturu, sun ceto wata jaririya da aka kiyasta kwananta daya da haifuwa .

A cewarsa nan da nan aka kai jaririyar sashin kula da jarirai na musamman, da ke Babban Asibitin Damaturu, inda gwajin lafiya ya tabbatar da cewa tana cikin koshin lafiya.

Daga baya aka kai ta ga sashen kula da jin daxin Jama’a don samun kulawa da kariya mai kyau, yayin da aka fara bincike don gano mahaifiyar da musabbabin jefar da jaririyar.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Usman Kanfani Jibrin ya umarci jami’an rundunar da su ci gaba da yin aiki tukuru a ci gaba da yaki da ayyukan ta’addanci a fadin jihar.

CP Usman ya kara godiya ga jama’a da kungiyoyin ’yan banga saboda ci gaba da goyon baya da hadin gwiwa da suke yi da hukumomin tsaro.

Rundunar ta yi kira ga mazauna yankunan jihar da su kasance masu yin taka tsantsan tare da ci gaba da ba da bayanai masu amfani a kan lokaci don taimakawa kokarin ’yan sandan.