An tsinci kwalba a kogi dauke da sako mai shekara 40

Da alama an jefa kwalbar ce tun a 1984

An tsinci kwalba a kogi dauke da sako mai shekara 40

Wani matukin jirgin ruwa a kogin Louisiana da ke kasar Amurka ya tsinci wata kwalba dauke da sako mai shekara 40 inda ya ci sa’ar gano wanda ya rubuta sakon.

Mutumin mai suna Jeremy Weir na yankin Coast, a Mississippi, ya ce yana cikin tukin jirgin ruwa a kogin Pearl kusa da Bogalusa a Louisiana sai ya hango wata tsohuwar kwalbar giyar Grolsch a cikin ruwan.

Mista Weir ya tafi da kwalbar zuwa gidansa, inda matarsa ta fahimci akwai wani abu a cikinta.

Sai ta bude kwalbar ta iske sakon da aka rubuta da hannu da wani yaro dan shekara uku mai suna Dabid Blanks ya yi.

Ga dukkan alamu an rubuta sakon ne tare da taimakon dangin Blanks a ranar 4 ga Yunin 1984 kuma yana dauke da lambar tarho da har yanzu iyayensa suna amfani da shi.

Iyayen Blanks sun ba Mista Weir lambarsa ta yanzu inda ya kira sakon yaron da yanzu ya zama magidanci.

Blanks ya tuntubi danginsa da suke tare lokacin da ya jefa kwalbar a cikin ruwa, kuma an gaya masa an jefa kwalbar ce a kusa da birnin Pearl River, kimanin mil 35 daga inda Mista Weir ya tsince ta.

Mista Weir ya ce yana son ya gana da Blanks nan ba da jimawa ba domin mika masa kwalbar da sakon.