An tsinci kwarangwal din yaro a cikin buhu

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka tsinci kasusuwan gawar wani yaro mai suna Mustafa Zubairu a bayan kurkukun garin Kafanchan bayan wata uku da bacewarsa. Mustafa, dan kimanin shekara takwas a duniya ya bata ne mako biyu kafin Babbar Sallar da ta gabata, inda ya fita gida bayan ya dawo daga Sallar Juma’a ya […]

An tsinci kwarangwal din yaro a cikin buhu

Marigayi Mustafa Zubairu da aka gano qwarangwal xinsa a Kafanchan

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka tsinci kasusuwan gawar wani yaro mai suna Mustafa Zubairu a bayan kurkukun garin Kafanchan bayan wata uku da bacewarsa.

Mustafa, dan kimanin shekara takwas a duniya ya bata ne mako biyu kafin Babbar Sallar da ta gabata, inda ya fita gida bayan ya dawo daga Sallar Juma’a ya ci abinci ya kuma fita, tun daga nan ba a sake jin duriyarsa ba.

Dan uwan mahaifiyar marigayin, Malam Abubakar Musa, ya ce yaron ke maraya ne da ya rasa iyayensa biyu kimanin shekara hudu da suka wuce. Kuma ya bayyana wa Aminiya cewa a ranar da abin zai faru ana yi masa aiki a dakinsa, sai yaron ya shigo inda ya ce ya fita waje.

“Abu kamar wasa shiru-shiru bai dawo ba, hankali bai fara tashi ba sai da magariba ta yi. Bayan karfe tara na dare zuwa goma ne aka tabbatar cewa lallai babu lafiya,” inji shi.

Abubakar ya ce sun binciki makwabta da gidajen ’yan uwa na kusa da nesa amma babu labari, abin da ya sa suka nemo mai shela ya zagaya cikin garin Kafanchan yana cigiya washegari kuma suka sanar da ’yan sanda.

“Amma tun daga lokacin babu wani labari sai yanzu kusan wata uku da aka tsinci gawarsa a cikin buhu ya zama kwarangwal. Ta hanyar tufafinsa da rigarsa da aka gani cikin buhun ne ya sa aka gane shi, domin babu komai a jikinsa sai kasusuwa. Ba mu taba ganin irin wannan ya faru a Kafanchan ba,” inji shi.

Kakar yaron wadda kuma yake hannunta bayan rasuwar iyayensa, Malama A’isha Musa, ta ce ta shiga dimuwa sosai bayan an zo an shaida mata cewa ta zo ta ga ko kokon kai da kwarangwal din jikanta da ya bace.

“Tunda ya fita bai dawo ba, hankalinmu ya tashi, mun baza cigiya har rafuka an je da masunta ko ya fada ruwa ne duka babu labari sai kawai ga wannan mummunan labarin bayan wata uku. Bayan Sallar Isha’i muka je muka duba, muka gane shi ne, ta hanyar tufafinsa da takalminsa da aka kunshe a cikin buhu. Daga nan aka kira ’yan sanda su gani, sannan aka kwashi kasusuwan aka je aka binne a cikin dare,” inji ta.

A wanin labarin kuma, kwana daya bayan gano kwarangwal din wancan yaron, an tsinci gawar wani magidanci mai kimanin shekara 44 a shagon aikinsa na kafinta.

Mamacin, mai suna Zakka Dawai, mai ’ya’ya biyu, dan kabilar Chawai ne da ke zaune a Unguwar Bayan Loko, Kafanchan, ba a san abin da ya yi ajalinsa ba, sai dai wadansu daga cikin ’yan uwansa sun shaida wa Aminiya cewa dama yana da hawan jini da ciwon olsa.

Wani makwabcinsa mai sana’ar gasa nama, ya ce kafintan mutumin kirki ne wanda ba a san shi da tashin hankali ba. “A ranar da abin ya faru, mun dauka ya fita ne, amma da muka ga dare ya fara yi shiru-shiru bai dawo ba, sai na ce a kulle masa shagonsa, aka kulle. Amma  har zuwa wayewar gari ko an kira a wayarsa ba a amsa, da aka zo shagon sai aka same shi ciki a mace kamar yana barci kuma babu wani alamar duka ko shaka ko kwarzane a jikinsa,” inji shi.

Wani makwabcin wurin mai sana’ar sayar da waya ya ce ganin haka sai nan da nan suka garzaya zuwa ofishin ’yan sanda na Kafanchan inda suka sanar da su halin da ake ciki, daga baya ’yan uwan mamacin suka zo suka tafi da gawar zuwa dakin ajiyar gawarwaki na asibitin Kafanchan.