An tsinci ’yar shekara tara da aka sato daga Katsina a Abuja
Wata yarinya mai kimanin shekara tara da haihuwa mai suna Maryam Adamu da ta ce ita ’yar unguwar Nasarawa ce a cikin birnin Katsina ta samu kanta a Abuja, bayan da wasu mata suka sato ta daga Katsina. A zantawa da Aminiya ’yarinyar wadda yanzu aka kai ta gidan wani mai unguwa a kauyen Tungan-Makama […]
Wata yarinya mai kimanin shekara tara da haihuwa mai suna Maryam Adamu da ta ce ita ’yar unguwar Nasarawa ce a cikin birnin Katsina ta samu kanta a Abuja, bayan da wasu mata suka sato ta daga Katsina.
A zantawa da Aminiya ’yarinyar wadda yanzu aka kai ta gidan wani mai unguwa a kauyen Tungan-Makama a karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja, an tsince ta ne a kusa da garin Deidei, Abuja a ranar Lahadin makon jiya, kuma ta ce wasu mata biyu ne suka dauko ta a mota bayan mahaifiyarta ta aike ta ta sawo itace, sannan suka yi watsi da ita. Wadanda ke rike da ita sun ce da farko sun yi shawarar tura ta Katsina amma saboda ba su da tabbacin akwai unguwa mai suna Nasarawa a birnin Katsina, sai suka jinkirta tura ta.