An tsinci yaro a iyakar Bauchi da Jigawa
Fadar Sarkin Nasaru da ke karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi ta ce an tsinci wani yaro da aka sato daga wani wuri aka jefar da shi a kan iyakar Jihar Bauchi da Jigawa.Yaron wanda yake ta kai-kawo a tsakanin garuruwan Sara zuwa Babaldu a Jihar Jigawa daga bisani fadar Sarkin Nasaru ta rike shi […]

Fadar Sarkin Nasaru da ke karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi ta ce an tsinci wani yaro da aka sato daga wani wuri aka jefar da shi a kan iyakar Jihar Bauchi da Jigawa.
Yaron wanda yake ta kai-kawo a tsakanin garuruwan Sara zuwa Babaldu a Jihar Jigawa daga bisani fadar Sarkin Nasaru ta rike shi yanzu kusan wata tara ana neman iyayensa.
Ciroman Nasaru Malam Garba Idi ne ya shaida wa wakilinmu haka a garin Nasaru, inda ya ce sun yi yawo da yaron wanda ya ce sunansa Kabiru mai kimanin shekara 10 har sun gaji ba tare da gano iyayensa ba.
Ya ce sun samu bayanin an sato yaron ne daga Rijiyar Malam da ke iyakar karamar Hukumar Bauchi da ta Toro a Jihar Bauchi, kuma an shaida musu cewa daga Miri a karamar Hukumar Bauchi aka dauko shi, amma duk an je can ba a samu iyayensa ba. Har ma wasu yankuna na Jihar Jigawa duk an kai yaron ba wanda ya ce ya san shi.
Ciroman Nasaru, ya ce a lokacin da suka tsinci yaron baya iya magana kuma sun dauki tsawon watanni suna yi masa jinya har ya dawo cikin hayyacinsa ya fara magana irin ta bebaye daga bisani ya yi bayyana musu cewa sunansa Kabiru, kuma sunan mahaifinsa Umaru, mahaifiyarsa kuma Zainab. Ya ce shi kadai ne a wurin mahaifinsa, a baya yana da kane amma ya rasu.
Ciroman ya kara da cewa yanzu yaron yana iya magana sai dai ba ya iya tuna inda ya fito da abubuwan da suka faru a baya gare shi. “A halin da ake ciki mun sanya yaron a makarantar firamare ta garin Nasaru kuma muna kokarin ganin an samu yadda za a sanya shi don ya kama sana’a ya iya rike kansa, amma muna neman kafafen watsa labarai su taimaka mana wajen gano iyayensa da ake zaton za su iya kasancewa daga jihohin Bauchi ko Kano ko Jigawa ko Adamawa ko Yobe,” inji shi.
Ya ce akwai alamun Kabiru asalinsa zai iya zama kabilar Babur ko Babarbare saboda wasu tsaga da ke fuskarsa, kuma baki ne dogo mai yawan fara’a.