An tsinto gawarwakin mutanen da suka yi hatsarin kwalekwale

An gano gawarwaki shida an kuma ceto mutum bakwai da ransu daga cikin mutanen da hatsarin kwalekwale ya rutsa da su a kan teku a cikin dare a jihar Legas. Fasinjoji 22 ne a cikin kwalekwalen da ya yi kife sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya a kan hanyarsa ta zuwa Ikorodu daga gabar ruwa […]

An tsinto gawarwakin mutanen da suka yi hatsarin kwalekwale

Wani karamin jirgin ruwan da ya yi hadari

An gano gawarwaki shida an kuma ceto mutum bakwai da ransu daga cikin mutanen da hatsarin kwalekwale ya rutsa da su a kan teku a cikin dare a jihar Legas.

Fasinjoji 22 ne a cikin kwalekwalen da ya yi kife sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya a kan hanyarsa ta zuwa Ikorodu daga gabar ruwa ta Ebute-Ero a daren Juma’a.

“Ana ci gaba da neman matukin jirgin da mataimakinsa da fasinjoji bakwai da suka cike adadin zuwa 22, maimakon 14 da ya kamata a dauka a tsarin COVID-19 na bayar da tazara”, inji Nosa Okunbor, kakakin hukumar agaji ta jihar Legas (LASEMA).

Ya ce gawa shida da aka gano duk mata ne, mutum bakwai da aka ceto a raye kuma sun hada da mata hudu da maza uku, yayin da LASEMA da hukumar albarkatun ruwan jihar (LASWA) da sauransu ke ci gaba da aikin ceto.

Wata majiya ta ce, “Duk da gargadin da ake wa masu kwalekwale su daina aiki a cikin dare, mai jirgin ya kama hanya a cikin rashin kyan yanani”.

LASWA ta ce tana kan bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin ruwan, kuma za ta hukunta duk wanda da samu da saba dokar hana tafiya a kan teku a cikin dare.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno