An tube wa ’yan sanda 5 kaki kan kwatar kudi a shingen bincike

Ana zargin su da karbar cin hancin Naira miliyan uku daga hannun wani mutum a Jihar Kuros Riba

An tube wa ’yan sanda 5 kaki kan kwatar kudi a shingen bincike

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta tube wa wasu jami’an ta biyar kaki sakamakon zargin su da karbar cin hancin kudi kimanin Naira milyan uku.

Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda mai kula da Shiyya ta shida ta da ke Jihar Kuros Riba, Jonathan Towuru, ya sanar a Kalaba cewa ’yan sandan sun kwace kudin ne da bakin bindiga a hannun wani mai abin hawa.

A makon jiya ne aka zargi jami’an da kwayar kudin da bakin bindiga a hannun wani mutum da rundunar ta sakaya sunansa.

Yanzu haka wadanda ake zargin an tube masu kaki amma ana tsare da su ana bincike, da zarar an same su da laifi kotu za a turasu ta yanke masu hukuncin da ya dace.

Mataimakin shugaban ’yan sandan ya ce wadanda ake zargin su da karbar cin hancin kudi Naira milyan uku daga wannun wani.

Ko a kwanan baya irin haka ta taba faruwa a kan babbar hanyar Kalaba zuwa Ikom inda aka kama wasu ’yan sanda kan karbar na goro.

Tafiya a kan hanyar na yawan zargin ’yan sanda da kula da shingen bincike a kan hanyar da yawan tatsar su kudi.