An tuhume su kan daura aure a kan aure
Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dala a Jihar Kano ta kama iyayen wata amarya mai suna Binta Sa’idu bisa daura mata aure a kan aure.Dangin mahaifiyar amaryar da yayan mahaifinta sun daura mata aure da wani mai suna Lawal Abdurarzak da ke Kaduna mako daya bayan mahaifinta ya daura mata aure da Mustapha Adamu da […]
Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dala a Jihar Kano ta kama iyayen wata amarya mai suna Binta Sa’idu bisa daura mata aure a kan aure.
Dangin mahaifiyar amaryar da yayan mahaifinta sun daura mata aure da wani mai suna Lawal Abdurarzak da ke Kaduna mako daya bayan mahaifinta ya daura mata aure da Mustapha Adamu da ke zaune a Farin Ruwa a karamar Hukumar Shanono a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne dalilin rabuwar aure a tsakanin iyayen amaryar wanda hakan ya sa Bintan ta bar garinsu na Farin Ruwa ta koma hannun yayarta da ke aure a Kaduna, inda Allah Ya hada ta da Lawal. Sai dai da ma tun kafin Binta ta koma Kaduna mahaifinta ya zaba mata miji wato Mustapha Adamu Farin Ruwa da ke gudanar da harkokin kasuwanci a birnin Kano.
Mahaifin Binta, Malam Sa’idu Idris ya yi mata baiko da Mustapha ya ci gaba da neman aurenta har aka sa musu rana. Kuma da lokaci ya matso sai ya nemi ta dawo hannunsa don yin biki inda aka daura mata aure da Mustapha a ranar 23 ga watan Janairu a kan sadaki Naira dubu 70.
Sai dai bayan daura mata aure da ’yan kwanaki sai mahaifiyarta mai suna Zainab da ke aure a Gashuwa ta Jihar Yobe ta nemi tsohon mijinta ya ba ta Binta ta tafi da ita can don yi mata shirye-shiryen gyaran aure inda mahaifin ya amince.
Amma washegari sai ta gayyaci yayan mahaifin Binta, Malam Muhammad Idris a kan zai yi wa yarinyar walicci a auren da za a daura mata a Kaduna inda kai tsaye ya amince ya tafi Kaduna tare da hadin kan mijin yayar Binta ya daura mata wani auren da Lawal Abdurrazak a ranar 28 ga Janairu, kuma nan take ta tare a gidan miji na biyu.
Bayan kwana takwas da tarewar ce, mahaifinta ya samu labarin inda ya shigar da kara gaban Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dala, wadda ta aike da sammaci ga wadanda ake zargi.
Sai dai lokacin da aka tuhumi yayan mahaifin Binta da mahaifiyarta da mijin yayarta da shi kansa mijin na biyu da laifin daura aure akan aure sun nemi Hukumar Hisba ta yi musu afuwa, inda suka ce sun yi haka ne bisa bin ra’ayin yariyar.
Da aka waiwayi Binta, ta ce tun farko ta sanar da mahaifinta cewa ba ta son Mustapha. “Dama ni ba na son Mustapha kuma mahaifina yana sane da hakan, don haka ni har yanzu ba na son sa da aure,” inji ta.
Jin haka sai Mustapha ya ce ya hakura da auren tunda ta ce ba ta son sa sai a biya shi kudin aurensa da sauran hidindimun da ya yi na auren.
Mataimakin Kwamandan Hisba na karamar hukumar, Abubakar Mati Salihu, ya shaida wa Aminiya cewa sun umarci Binta ta zauna ta yi istibira’i kafin a sake daura mata aure da mijinta na biyu wato Lawal.