An tuhumi matasa biyu da boye matar aure a Zariya
Wata babbar kuton Shari’ar Musulunci da ke Tudun Wada Zariya ta tasa keyar wasu samari biyu zuwa gidan yari domin zaman wakafi na mako biyu a kan tuhumarsu da hada baki wajen boye matar aure da yin lalata da ita na tsawon kwanaki biyar. Mai gabatar da kara Sajen Adamu Yahaya ya gabatar da wadanda […]

Wata babbar kuton Shari’ar Musulunci da ke Tudun Wada Zariya ta tasa keyar wasu samari biyu zuwa gidan yari domin zaman wakafi na mako biyu a kan tuhumarsu da hada baki wajen boye matar aure da yin lalata da ita na tsawon kwanaki biyar.
Mai gabatar da kara Sajen Adamu Yahaya ya gabatar da wadanda ake tuhuma, Usman Yusuf da Rabi’u Muhammadu. Ya ce abin da suka aikata laifi ne da ya saba ma sashi na 280 da 122 da kuma 178 kundin Shari’a na SPC.
Wadanda ake tuhuma da aikata laifin, na farko mai suna Usman Yusuf ya amsa laifinsa, inda ya ce shi ne ya dauko ta ya kai ta dakin abokinsa da ke Layin Nabawa Tudun Wada, kuma ya yi ta lalata da ita. Shi kuma abokinsa mai suna Rabi’u Muhammadu ya ce shi bai san matar aure ba ce kuma bai yi lalata da ita ba.
Alkalin kotun Aminu Sa’ad ya tura su zaman wakafi har na mako biyu kafin a kammala bincike kuma ya ba da umurni a kai matar asibiti, domin a bincike ta ko tana da ciki kafin a dawo.
Wakilin Aminiya ya ji ta bakin matar mai suna Amira Usman, domin jin abin da ya haifar da haka sai ta ce: “Mun samu rashin jituwa ne da mijina, shi ne na fita cikin dare domin zuwa gida sai na hadu da shi, sai na bi shi.