An tuhumi matashi da lalata da kaza a Akure
Wani matashi dan shekara 19, mai sana’ar walda a Akure ta Jihar Osun, an kamka shi ya yi wa kaza fyade har sai da ta mutu. Wanda ake zargi da aikata wnanan laifi, a garin Afo da ke karamar Hukumar Ose, ya aikata laifin ne da karfe 11 da minti 20 na dare, inda makwafciyarsa, […]
Wani matashi dan shekara 19, mai sana’ar walda a Akure ta Jihar Osun, an kamka shi ya yi wa kaza fyade har sai da ta mutu. Wanda ake zargi da aikata wnanan laifi, a garin Afo da ke karamar Hukumar Ose, ya aikata laifin ne da karfe 11 da minti 20 na dare, inda makwafciyarsa, Misis Stella Akintola ta bayar da shaidar cewa ya aikata laifin.
A cewarta, ta kwanta da wuri, sai akwai karar ighun kaza ya farkar da ita, inda ta gano cewa llaai wani abu yana damun kazar. Sai ta fita, in data ga kofar waje a bude.
“Sai na yi kira da karfi ko wane ne a baya, nan take nag an shi ya fito daga sakon gidan, yana cewa ya je kasha ne, domin cikinsa na murdawa,” inji shi. Misis Akintola ta ce ba ta gamsu ba, musamman da ta fahimci karar da kazar take yi ta daina. Sai akwai ta tafi wurin da kazar take, amma ba ta ga komai ba. “da na shiga bayan daki, sai na ga daya daga cikin kaji a mace, inda gashinta ya bata kasan wurin,” inji ta. Ta ce, duk da cewa ba ta fahimci cewa shi ya kashe kazar ba, sai akwai ta yi masa ihu, har ya yi ikrarin aikata laifi.
Akintola ta ce, wanda ake zargi da aikata laifin ya tabbatar da laifinsa, sannan ya roketa ta yafe masa, inda ya yi alkawarin biyan kudin kazar da ta mutu. Ta ce ta yanke cewa ba za ta sanar da ’yan sanda ba, saboda ba za ta iya jure wa wahalar kai kawo zuwa wajen ’yan sanda kan wannan “dan karamin laifi.” “rahotannin sun samu hujojin da ke tabbatar da cewa mutumin ya yi lalata da kazar, a lokacin da mai kazar ta dubata, tare da sauransn mutanen gidan.” A cewar rahotanni.
Shaidanu ne suka ingiza ni, a cewar wanda ake tuhuma, kamar yadda ya bayyana wa manema labarai. Ya ce: “Ina cikin barci sai wani ruhi ya zo wajena, ya umarceni in je bayan gida. Dagan an ban san halin da nike ciki ba, har sai da na samu kaina a halin lalata da kaza.”
Da aka tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda, Wole Ogodo, sai ya ce, tunda aka kawo rahoton al’amarin ga ’yan sanda, ba zai iya yin wani sharhio a kai ba. Ogodo ya yi nuni da cewa: “Wani al’amari ne da al’ummar ta gabatar mana don mu yi bincike. Wannan sabon al’amari ne, idan har abin da kuka gaya mini ya zama gaskiya.