An tuhumi matashi da yunkurin kashe mahaifinsa da kannensa

Wani matashi mai suna Murtala Abubakar ya gurfana a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci ta Gyadi-gyadi bisa zargin yin barazanar kisa ga mahaifinsa da kuma kannensa guda biyu.dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotu cewa mahaifin matashin ne mai suna Abubakar Aminu ya kai karar matashin a gaban ’yan […]

An tuhumi matashi da yunkurin kashe mahaifinsa da kannensa
An tuhumi matashi da yunkurin kashe mahaifinsa da kannensa

Wani matashi mai suna Murtala Abubakar ya gurfana a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci ta Gyadi-gyadi bisa zargin yin barazanar kisa ga mahaifinsa da kuma kannensa guda biyu.
dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotu cewa mahaifin matashin ne mai suna Abubakar Aminu ya kai karar matashin a gaban ’yan sanda, inda ya ce a daren Litinin da ta gabata, dan nasa ya zare wuka da nufin zai yanka shi da kannensa mai suna Umar Abubakar da A’isha Abubakar.
Har ila yau, dan sandan ya bayyana cewa laifin da ake zargin matashin da shi laifi ne da ya saba da sashe na 227 na kundin shari’a na finalkod.
Sai dai wanda ake zargin bai amsa laifinsa kai tsaye ba, inda ya bayyana wa kotu cewa wasu kudi yake bin kanin nasa bashi wanda shi kuma ya ki biyansa. Haka kuma a waje daya mahaifin nasu yana goyon bayan kanin nasa a duk lokacin da wata rigima ta shiga tsakaninsa da su, musamman ma abin da ya shafi kudi.
Alkalin kotun, mai shari’a Kabir Imam ya bayar da umarnin tsare matashin a gidan maza tare da dage shari’ar zuwa ranar 10 ga watan gobe don ci gaba da sauraren shari’a.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi