An tuhumi mawaki Chris Brown da fasa wa wani hanci
A ranar Lahadi da ta gabata ce ’yan sanda a Washington DC suka kama mawaki Chris Brown, suka sakaya shi saboda laifin fasa wa wani mutum hanci.An kama mawakin ne, bayan da wani mutum ya kai karar mai kula da lafiyarsa tare da shi kansa, cewa sun fasa masa hanci a bakin kofar shiga wani […]


A ranar Lahadi da ta gabata ce ’yan sanda a Washington DC suka kama mawaki Chris Brown, suka sakaya shi saboda laifin fasa wa wani mutum hanci.
An kama mawakin ne, bayan da wani mutum ya kai karar mai kula da lafiyarsa tare da shi kansa, cewa sun fasa masa hanci a bakin kofar shiga wani otel mai suna W Hotel.
’Yan sanda sun sallami mawakin ne a ranar Litinin da ta gabata, bayan ya kwana daya a komarsu, inda ake sa ran nan gaba za a shiga kotu domin fara shari’a. Kamar yadda doka ta tanada, idan kotu ta kama shi da laifi, zai fuskanci daurin watanni shida cur a gidan yari.
Mawakin dan shekara 24, ya samu kariya daga lauyansa, Danny Onorato, wanda ya ce mai kula da lafiyar tasa ya yi amfani da karfi ne wajen gudanar da aikinsa, kamar yadda dokar Yankin Columbia ta ba shi iko. “Christopher Brown bai aikata wani laifi ba. Mun fahimci cewa mai kula da laifiyarsa ya yi amfani da karfi ne domin gudanar da aikinsa na kare lafiyar Chris da dukiyarsa, kamar yadda dokar Yankin Columbia ta ba shi ikon yin haka. Muna da tabbacin cewa mawakin bai aikata wani laifi ba, don haka za a wanke shi daga duk wata tuhuma.” Inji lauyan mawakin.
Kamar yadda takardun kotu suka nuna, mutumin da aka fasa wa hanci, Parker Adams, dan shekara 20 da haihuwa, ya shaida wa ’yan sanda cewa, yana tafiya ne sai ya gitta ta inda Chris Brown ke daukar hoton wata mata da saurayinta, inda mawakin da kuma mai kula da lafiyarsa, Chris Hollosy suka far masa da duka. Daga bisani kuma mawakin da tawagarsa suka shige mota suka bar wurin.
Ana sa ran mawakin zai sake bayyana a kotu a ranar 25 ga watan nan.
Mawaki Chris Brown dai ya yi kaurin suna wajen dukan mutane. A 2009, ya taba yi wa tsohuwar farkarsa, Rihanna duka kuma aka yanke masa hukuncin jeka-da-halinka na tsawon shekara biyar. Haka kuma, a watan Agustan da ya gabata, duk da an wanke shi daga laifi, an zarge shi da bangaje motar wata mata. Haka ma a watan Janairu na bana, an samu labarin cewa ya yi fada da mawaki Frank Ocean a dalilin wurin aje mota a bakin shagon daukar waka a Hollywood.
Mawaki Chris ya samu an sallame shi ne, kasancewar mawaki Frank ya nuna cewa ba ya son su yi shari’a.
Ya zuwa yanzu, mawaki Chris na gab da fitar da sabon faifan wakokinsa mai taken ‘d’