An tuhumi wadansu da laifin fille kan jaririnsu a Ghana
Ma’aurata a wata unguwa da ake kira Anumle da ke kusa da makarantar Achimota a kasar Ghana sun fada komar jami’an tsaro bayan an zarge su da laifin halaka jaririnsu dan wata biyu a kokarin da suke na yin tsafi da shi don su samu kudi. Mutumin mai suna Yaw Grushie wanda ke aiki a […]
Ma’aurata a wata unguwa da ake kira Anumle da ke kusa da makarantar Achimota a kasar Ghana sun fada komar jami’an tsaro bayan an zarge su da laifin halaka jaririnsu dan wata biyu a kokarin da suke na yin tsafi da shi don su samu kudi.
Mutumin mai suna Yaw Grushie wanda ke aiki a makarantar Achimota shi da matar sa, an zarge su ne da fille kan jaririnsu suka sayar akan sidi dubu 10 kwatankwacin Naira miliyan 1 da dubu 250 amma aka fara biyansu sidi dubu 2 kwatankwacin Naira dubu 250 sa matsayin somin-tabi.
Wadanda aka yi abin a kan idonsu a harabar makarantar sun ce ma’auratan sun amsa laifinsu bayan an tursasa musu, inda yanzu haka suke nadamar aikata wannan abin kunya. Sai dai jami’an tsaro suna tsaurara bincike don gano dalilin da ya sa suka aikata haka da kuma wanda ko wadanda ke da hannu a cikin wannan mummunan aiki.
Bincike ya nuna garin Anumle da kuma wasu garuruwan da ke kusa da shi da suka hada da kauyen Christian da na Kisseman sun yi kaurin suna wajen tattara batagari musamman masu neman yin kudi a dare daya ta hanyar damfara da kuma yin tsafi abin da ake wa lakabi da Sakawa a Ghana.