An tunatar da ’yan Arewa da ke Kudu muhimmancin zaman lafiya

Shugaban al’ummar Arewa mazauna Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh, ya bukaci su zauna lafiya da wadanda suke tare,  inda ya fara bayaninsa da yin kira tare da Shawartar ‘yan Arewan akan batun zaman lafiya, cewa: ‘’Zaman lafiya shi ne abu mafi muhimmanci da ya wajabta mu tabbatar kafin komai, don haka ‘yan Arewa mazauna jihar […]

An tunatar da ’yan Arewa da ke Kudu muhimmancin zaman lafiya
An tunatar da ’yan Arewa da ke Kudu muhimmancin zaman lafiya

Shugaban al’ummar Arewa mazauna Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh, ya bukaci su zauna lafiya da wadanda suke tare,  inda ya fara bayaninsa da yin kira tare da Shawartar ‘yan Arewan akan batun zaman lafiya, cewa: ‘’Zaman lafiya shi ne abu mafi muhimmanci da ya wajabta mu tabbatar kafin komai, don haka ‘yan Arewa mazauna jihar Edo da sauran jihohin Kudu su hada kai, tare da  kusantar hukuma da shagabannin gargajiya, domin hada kai da sarakuna da kusantuwa ga hukuma yana da amfani. Kuma ina shawartar duk wani dan Arewa a nan kudu ko Arewa, da ya mutunta kansa ya siffantu da siffar mutanen kirki, kuma ya nisanta kansa daga neman fitina, ko tada zaune tsaye, su kuwa Shugabanni da suke a Arewa wajibi ne su tashi tsaye wajen fadakar da matasa muhimmancin zaman lafiya’’.
 Sarkin Hausawa na Benin Alhaji Isah Adamu,  ya bayyana matukar damuwarsa game da guje-gujen da ‘yan Arewa ke yi a duk lokacin da aka fuskanci lokaci irin wannan, inda suke mayar da kawunansu tamkar ba ‘yan Najeriya ba, alhali ko wadanda ba ‘yan kasar nan ba ba su nuna irin wannan dabi’ar, inda suke tafiyar da harkokinsu tamkar ‘yan kasa.
“Ssaboda wannan ina kira ga daukacin ‘yan Arewa mazaunan Jihar Edo da yankin Kudu baki daya, da su san cewa ko’ina akwai Allah, kuma shi ne mai kare bayinsa a duk inda suke. Don haka kada su manta da Allah da ya yi su suna biye wa zukatansu, inda masu raunin imani ke rikita musu hankali. Sai a fahimci irin wadannan  mutane su ne kishiyoyin zaman lafiya a kasar nan da al’ummarta. Najeriya ce kasar ‘yan Najeriya,”  inji shi.
 Shima Sarkin Nufawa, Alhaji Idiris Sani, a shawarar da ya bai wa al’ummar Arewa, da farko ya ce ‘yan Arewa mazauna Kudu mu yi hakuri da juna da kuma sauran abokan zamanmu na Kudu; mu yi zama irin na ‘yan uwan juna kuma a daina yin anfani da shaci fadi, ko yada jita-jita mara tushe da za su tayar da zaune tsaye, musamman masu gudu suna komawa Arewa akan batun zaben kasar nan.
“ Ya kamata irin wadannan mutane su san irin bayanan da za su  yada wa ‘yan uwansu a Arewa. Don haka, ina kira ga ‘yan Arewa mazauna Kudu akan su hada kansu, tare da aikata abin da zai kawo alheri. Kuma ina rokon shugabannin tsaro su dauki matakan tsaro na kare jama’a, ba sai sun jira har komai ya baci ba. Su ma sarakunan gargajiya, ina kiransu a kan hadin kai da tunkarar matsalolin al’ummarsu, da yin adalci game da aikin jama’a,” inji shi.
 Mai baiwa Gwamna Shawara akan harkokin da ya shafi rayuwar al’ummar Arewa mazauna Jihar Edo, Alhaji Sahabi Aliyu (J.P.),  a bayaninsa cewa ya yi:  ‘’ Ina son mutane su gane cewa zaman lafiyar kasa na rataye ne a wuyan kowane dan kasa. Saboda haka idan muka hada kanmu muka nuna muna son zaman lafiya, to, lallai da yardar Allah komai zai zama da sauki, amma irin wannan guje-gujen na babu gaira, babu dalili, ba za su kawo tsira ba; kawai muna son mu mayar da kanmu tamkar baki a yau muna Kudu; gobe muna Arewa. Ya kamata mu natsu. Ina ganin idan mun yi amfani da hakan zai kara ba mu zaman lafiya da hadin kai da duk wani dan Kudu a bangaren siyasa ko addini. Daga bisani ya bukaci jami’an tsaro, da su kara kokarin tsare rayuka da dukiya.
Sannan ya shawarci ‘yan uwansa ‘yan siyasa, da cewa,  su sanya tsoron Allah cikin ayyukansu na jama’a, tare  da cika alkawurra da yin adalci da aiki da gaskiya. Inda daga bisani ya ja kunnen matasa akan su guji tada zaune tsaye a lokacin zabe wannan shekara ta 2015.