An tura jami’an ‘yan sanda dubu Legas don magance cushewar ababen hawa

Rundunar ‘yan sandan Legas ta tura karin zaratan jami’anta dubu a sassan manyan titunan Legas, domin magance cunkoson ababan hawa da ake fama da shi a ‘yan kwanakin nan a jihar Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Hakim Odumosu, ne ya bayyana hakan a wani taron gaggawa da ya kira a hedwatar rundunar da ke Ikeja […]

An tura jami’an ‘yan sanda dubu Legas don magance cushewar ababen hawa

Rundunar ‘yan sandan Legas ta tura karin zaratan jami’anta dubu a sassan manyan titunan Legas, domin magance cunkoson ababan hawa da ake fama da shi a ‘yan kwanakin nan a jihar

Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Hakim Odumosu, ne ya bayyana hakan a wani taron gaggawa da ya kira a hedwatar rundunar da ke Ikeja a yau Laraba domin lalubo bakin zaren magance cunkoson ababan hawa a birnin na Legas.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kira taron ne cikin kwanaki biyu da ya fara jan ragamar Rundunar ‘yan sandan a jihar Legas inda ya zayyana daukar matakan kattakwana akan cinkoson ababan hawa a Legas, taron da ya sami halartar manyan jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sassa daban daban na jihar.

A baya bayan nan cunkoson ababan hawa ya kara yin tsamari a birnin Legas inda jama’a da dama suka gwammace yin tafiya a kasa maimakon su hau mota zuwa wajen aikin su ko fita gudanar da al’amuransu na yau da kullum.

Lokacin taron