’Yan Najeriya da suka kamale a Ukraine za su iso gida ranar Alhamis

Rukunin farko na ’yan Najeriya da suka makale a Ukraine bayan barkewar yaki za su iso gida ranar Alhamis 3 ga Maris, 2022.

’Yan Najeriya da suka kamale a Ukraine za su iso gida ranar Alhamis

Wasu dalibai da suka makale a iyakar kasar Ukraine da Poland, na zargin jami’an tsaron Ukraine da cin zali da kuma nuna wariyar ga baki. (Hoto: CNN).

A ranar Laraba Gwamantin Tarraya za ta fara kwaso dalibai da sauran ’yan Najeriya da suka makale a kasar Ukraine bayan yaki ya barke.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta sanar cewa jiragen kamfanoni Max Air da Air Peace na kan haryarsu daga Najeriya domin kwaso mutum 1,284 daga kasashen Hungary, Poland, Romania da Slovekia masu iyaka da Ukraine zuwa gida.

Ta sanar a safiyar Laraba cewa, “Rukunin farko da za a kwaso za su iso Najeriya ranar Alhamis 3 ga watan Maris, 2022,” kuma kawo yanzu ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen hudu sun karbi ’yan Najeriya 2,090 a kan iyakokin kasar bayan sun tsallako daga Ukraine.

Ma’aikatar ta hannun Babba Sakatarenta, Ambasada Gabriel Aduda, ta ba da lambar kar-ta-kwana ga masu neman agaji a kasashen waje kamar haka:+234 916 084 7498, +234 701 088 2907.

Ambasada Gabriel Aduda, ya ce, “Kawo yanzu mutanen da za a kwaso su hada da mutum 650 a kasar Hungary, 350 daga Poland, 940 daga Romania, da kuma 150 daga Slovakia.

“Jiragen da za su kwaso su da kuma adadin mutane da za a dauka su ne kamar haka: Max Air zai kwaso 560 daga Romania; Air peace kuma zai kwaso 364 daga Poland da wasu 360 daga Hungary,” inji Ambasada Gabriel Aduda.

Ya ce ma’aikatar tana yin duk mai yiwuwa, ba dare, ba rana, domin ganin duk ’yan Najeriya da suka malake a Ukraine sun dawo gida cikin aminci.