An tura matasa biyar zaman kaso kan yunkurin fyade ga budurwa

’Yan sanda sun gurfanar da wasu matasa biyar a gaban kotu bisa tuhumarsu da laifin yi wa wata budurwa da aka sakaya sunanta fyade a kauyen Illu da ke karamar Hukumar Kiyawa da ke Jihar Jigawa a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse. Budurwar mai shekara 14 ana zargin matasan sun kamata […]

An tura matasa biyar zaman kaso kan yunkurin fyade ga budurwa
An tura matasa biyar zaman kaso kan yunkurin fyade ga budurwa

’Yan sanda sun gurfanar da wasu matasa biyar a gaban kotu bisa tuhumarsu da laifin yi wa wata budurwa da aka sakaya sunanta fyade a kauyen Illu da ke karamar Hukumar Kiyawa da ke Jihar Jigawa a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse.

Budurwar mai shekara 14 ana zargin matasan sun kamata ta da karfin tsiya ne suka yi yunkurin lalata da ita a wani daji da ke tsakanin Kiyawa da garinsu da misalin karfe 10:00 na dare lokacin da take komawa gida.
Yarinyar ta ce a cikin matasan akwai Labaran Sale wanda ta ce shi ne ya rike ta sai
Hashim Iliya da ya fara neman yin lalata da ita, yayin da Shafi’u Ibrahim yake gefe a tsaye yana kallon yadda za ta kaya, inda ta yi ihu sai wasu matasa suka kawo mata agaji a inda aka kada ita a gindin wani itacen mangwaro.
Sai dai kuma a cewar daya daga cikin wadanda suka sun cece ta ne, mai suna Faruk Badamasi saboda dimaucewa ne ta sanya sunayensu a cikin wadanda suka yi yunkurin yi mata fyade.
Faruk Badamasi ya ce shi da Sani Isah da Aminu Ya’u ne suka kwace ta daga wajen matasan, amma sai ta sanya su a cikin matasan da suka yi yunkurin yi mata fyaden. Don haka ya roki kotu ta wanke su kan zargin domin taimako suka je ba yi wa yarinyar fyade ba.
Alkalin Kotun Malam Muhammed Mustapha ya tura matasan biyar zuwa gidan maza na mako biyu domin bai wa kotun damar nazarin shari’ar kafin ta yanke hukunci a kai.