An tura sojojin Najeriya samar da tsaro a Guinea-Bissau

Najeriya ta tura sojojinta zuwa kasar Guinea-Bissau domin samar da tsaro da magance rigingimun siyasa

An tura sojojin Najeriya samar da tsaro a Guinea-Bissau

Sojojin Najeriya 177 ne aka tura domin samar da tsaro da magance tashe-tashen hankulan siyasa a kasar Guinea-Bissau.

Sojojin da suka hada da hafsoshi 17 da sojoji 160, an tura su ne bayan da aka basu horo domin tunkarar aikinsu.

A yayin bikin yaye kamfanin na Najeriya Company 3 na kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afrika ta Yamma (ECOWAS) a Guinea Bissau, Manjo Janar Ademola Adedoja, kwamandan MALIPKC, ya ce horon da suka samu na da muhimmanci a ayyukan wanzar da zaman lafiya da ya dace da kalubalen tsaro na Guinea-Bissau.

“Sojojin sun samu cikakkiyar masaniya game da inda aka tura su, aikin da ke gabansu, manufarsa, halin da ake ciki yanzu,” Manjo Janar Adedoja ya bayyana.

Horowar ta haɓaka fahimtar sojojin da kuma shirye-shiryen ayyukansu samar da tsaro da aka tura su.

Haka kuma, horon ya haɗa da fasahohin zamani, ciki har da  sarrafa jiragen sama marasa matuki.

Manjo Janar Boniface Sinjen, babban hafsan rundunar sojin Najeriya, ya jaddada muhimmancin shigar Najeriya cikin aikin.

Ya jaddada kudirin Najeriya na tallafa wa kasar Guinea-Bissau wajen shawo kan tabarbarewar siyasa da rigingimu, wadanda ke barazana ga zaman lafiya da ci gaban yankin.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana