An tura su jarun akan lalata da juna
Reshe ya juye da mujiya inda wata mace mai kimanin shekara 35 da ta gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna saboda zargin yin lalata da saurayinta mai kimanin shekara 25.A takardar da dan sanda mai gabatar da kara Ahmad Musa ya karanta a gaban kotu, ya bayyana cewa matar mai […]
Reshe ya juye da mujiya inda wata mace mai kimanin shekara 35 da ta gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna saboda zargin yin lalata da saurayinta mai kimanin shekara 25.
A takardar da dan sanda mai gabatar da kara Ahmad Musa ya karanta a gaban kotu, ya bayyana cewa matar mai suna Talatu Sa’idu Getso ce da kanta ta kai karar abokin lalatarta ga ofishin ’yan sanda inda ta bayyana cewa masoyin nata mai suna Bello Ibrahim Panshekara ya sha yin lalata da ita, kuma a dalilin haka ne ta samu juna biyu har ta haifi jariri.
Sai dai kuma kotun ta tuhumi su duka biyun wato da mai zargin da wanda ake zargi da laifin fasikanci wanda ya saba wa sashi na 124 na kundin shari’ar Musulunci ta Jihar Kano na shekarar 2000.
Bayan karanta musu laifinsu a take mutanen biyu suka amsa laifinsu.
Alkalin kotun Mai shari’a Abubakar Ayagi ya bayar da umarnin tsare su a gidan kurkuku inda kuma ya dage saurarar shari’ar zuwa nan gaba.