An umarci limamai da su dakatar da jam’i a masallatai
Mai Martaba Sarkin Jama’a Alhaji (Dakta) Muhammad Isa Muhammad II, ya umarci dukkanin limaman da ke masarautarsa da su bi umarnin gwamnati da shawarwarin masana kiwon lafiya su guji tara mutane a masallaci don yin sallar jam’i domin kiyaye lafiyar jama’a da kare yaduwar cutar Covid-19 a cikin al’umma. Sarkin Jama’a ya yi wannan kiran […]
Mai Martaba Sarkin Jama’a Alhaji (Dakta) Muhammad Isa Muhammad II, ya umarci dukkanin limaman da ke masarautarsa da su bi umarnin gwamnati da shawarwarin masana kiwon lafiya su guji tara mutane a masallaci don yin sallar jam’i domin kiyaye lafiyar jama’a da kare yaduwar cutar Covid-19 a cikin al’umma.
Sarkin Jama’a ya yi wannan kiran ne a Fadarsa ranar Laraba yayin da ya yake zama tare da dukkanin shugabannin addini da malaman masallatan khamsus-salawat da ke cikin garin Kafanchan a jihar Kaduna.
Sarkin, ya ce rashin aikata hakan ba shi daga kishin addini face rashin kishin jama’a domin kuwa, babu wanda aka hana shi gudanar da addini sai dai nisantar da duk wani abu da zai haddasa cunkoson jama’a da suka hada da cin kasuwanni da tarukan daurin aure da kuma gudanar da sallolin jam’i.
Ya ce, bai kamata mutane su rika yin sakaci da cutar da aka tabbatar da bullarta kuma ake daukar matakai daban-daban ba dare ba rana don yaki da ita ba, sannan wasu su rika wasa da lamarin ba.
“Idan har kasar Saudiyya za ta dakatar da salloli a masallacin harami na Makka da Madina da kuma dakatar da sallar tarawi da tahajjud a watan Ramadan mai zai hana mu daukar irin wannan matakin don gujewa kamuwa ko yaduwar wannan cutar a cikin jama’a ba.” In ji shi.
- COVID-19: An killace mutum biyu a asibitin Kafanchan
- Ba alamar Coronavirus ga wadanda ake zargi a Kafanchan – Dakta Habila
A karshe ya roki jama’a da su yi hakuri kafin nan da lokacin da komai zai dawo daidai, inda ya bukaci mutane da su dage da yin addu’o’i tare da kiyayewa.
Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban ‘Yan Sandan yankin Jama’a (Area Commander), ACP Danladi Ibrahim ya ce bisa ga kallo da sauraron irin yadda cutar take da kuma irin illar da take yi a wasu wurare, ta hanyar kafafen hada labarai, bai kamata a samu wani mai sauran kokwanto game da wannan cuta ta Covid-19 ba, inda ya yi kira ga jama’a da su kiyaye tare da nisantar taruka domim a cewarsa, akwai barazanar fantsamar cutar cikin mutane musamman idan aka yi la’akari da wadanda ake zarginsu kuma suka tsere zuwa cikin jama’a ba tare da zuwa an gwada su don daukar mataki a kansu ba.
Da yake karin haske kan manufar taron, Lifidin Jama’a, Alhaji Basheer Idris, ya ce sakamakon zaman tsaro da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar ne aka zartar da dorawa mai martaba nauyin fadakar da mutane saboda ci gaba da kiyayewa lura da irin matsayin da yake da shi saboda ci gaba da kiyayewa. Don haka ya bukaci jama’a da su yi wa lamarin kyakkyawar fahimta.
A karshe Mallam Musa Abubakar Imam, ya roki musulmi da Kirista da su koma ga Allah ta hanyar istigfari da addu’o’i don neman mafita daga wannan annobar.