An wajabta wa mata Musulmi ’yan sakandare yin shigar Musulunci a Borno

Gwamnatin Borno ta wajabta yin lullubi ga ’yan mata Musulmai da ke makarantunta na sakandare a fadin jihar. 

An wajabta wa mata Musulmi ’yan sakandare yin shigar Musulunci a Borno

Gwamna Zulum yayin rijistar yaran makaranta

Gwamnatin Borno ta wajabta yin lullubi ga ’yan mata Musulmai da ke makarantunta na sakandare a fadin jihar. 

Daraktan Kula da Makarantu na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Borno, Bukar Mustapha-Umara, ya bayyana cewa, ƙarƙashin sabon tsarin, wajibi ne kowace ɗalibar sakandare Musulma ta sanya wando da riga da ɗankwali da lullubi a duk makarantar da take a fadin jihar.

“Wannan shigar ta zama wajibi ga dukkan ɗalibai mata Musulmi a duk makarantunmu na sakandare da ke Jihar Borno.

“Amma ga ɗalibai Kirista mata zaɓi ne; In sun so sa su iya kasancewa da shigar da suke da ita a yanzu ko kuma su canza wando kawai.”

Daraktan ya kara da cewa cewa wajibi ne shugabannin makarantun su tabbatar da bin ƙa’idojin sabuwar shigar.

Ya kuma bayyana cewa sabuwar dokar sanya tufafin dole ga ɗalibai Musulmi za ta fara aiki daga zangon karatu na farkon shekarar karatu ta 2023/2024 da ke tafe.

Sannan ya yi kira ga iyaye da su yi  cikakken shirin fara amfani da sabuwar shigar makarantar kafin a ahekarar karatu ta 2023/2024.