Za a biya ma’aikatan Gombe garatutin N3bn

Gwamnatin ta ce za ta biya hakkin ne don faranta wa ma’aikatan da suka ritaya.

Za a biya ma’aikatan Gombe garatutin N3bn

Gwamnatin Jihar Gombe ta shirya fara biyan hakkin ma’aikatan da suka yi ritaya a Kananan Hukumomi 11 na jihar.

Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomin jihar, Abdulkadir Waziri ne, ya sanar wa manema labarai jim kadan da kammala zaman Majalisar Zartarwar jihar karo na 36.

Ya ce gwamnati ta ware sama da Naira biliyan uku don fara biyan bashin giratutin baya zuwa shekarar 2022.

Har wa yau, ya ce wasu kananan hukumomin za su biya na shekara biyu wasu zuwa sama.

Waziri, ya kuma ce baya ga wannan majalisar ta amince wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, da ya gina gidajen sarakuna a wasu kananan hukumomi da samar musu da hanyoyi.

Kazalika, gwamnatin jihar za ta kashe kashi, na adadin kudaden da za a kashe wajen ayyukan yayin da kuma uma kananan hukumomin za su kashe sauran kudin.

Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe

Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara