An watsa wa dalibi ruwan batir a Zariya

Wani wanda ba a san ko wane ne ba ya watsa wa wani dalibi mai suna Zaharadin Ibrahim Raka ruwan batir a jikinsa. dalibin mai shekara 18  wanda yake zaune a gida Mai lamba 3 Layin Bako Zuntu Sabuwar Unguwa Zariya, dalibi ne a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a […]

An watsa wa dalibi ruwan batir a Zariya
An watsa wa dalibi ruwan batir a Zariya

Wani wanda ba a san ko wane ne ba ya watsa wa wani dalibi mai suna Zaharadin Ibrahim Raka ruwan batir a jikinsa.

dalibin mai shekara 18  wanda yake zaune a gida Mai lamba 3 Layin Bako Zuntu Sabuwar Unguwa Zariya, dalibi ne a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Aminiya ta ziyarci asibitin da dalibin yake kwance yana jinyar konewar da ruwan batirin ya yi masa, inda  yace “A ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe tara na dare na dawo makaranta zan shiga gida sai wani wanda ban san shi ba ya yi mini sallama, na amsa. Sai ya ce don Allah yana tambaya ne, sai na ce Allah Ya sa na sani. To, a nan sai muka tsaya yana kokarin tuna sunan wanda yake tambaya amma ya kasa. Muna tsaye da shi har kusan minti ashirin amma ya kasa tuno sunan wanda yake nema. Wai a cewarsa ya ba shi gyaran waya ne kuma ya nuna maasa gidanmu cewa nan ne gidan wanda yake nema.”

“To har na juya zan tafi sai ya kara kirana na dawo. Ina dawowa kawai sai na ji ya watsa mini wani abu mai zafi. Nan da nan ko’ina nawa ya kama zafi kamar wuta ta kama rigata. Sai na shiga gida da gudu ina ta salati ina kuka, shi kuma daga nan sai ya gudu,” inji shi.

Ya kara da cewa, “To daga nan ne aka kawo ni asibiti kuma ban san shi ba kuma ban yi fada da kowa ba, kuma ni ba ni da wani abokin gaba da zan iya cewa shi ne ya aikata mini haka. Sai dai ina zargin wani abokin yayana wanda har ya taba rubuto masa wasika ta waya cewa zai kashe shi, kuma a wancan lokacin ba mu dauki wani mataki ba. Shi yayan nawa malami ne, yana karantarwa ne; ka ji abin da zan iya tunawa.”

Mahaifin dalibin, Malam Ibrahim Zubairu ya ce, “Ba a gane wanda ya aikata wannan aiki na marasa imani ba, sai dai zargi amma Allah yana nan kuma za mu roke Shi, domin Shi Allah Ya san wanda Ya aikata hakan, kuma za mu ba ’yan sanda hadin kai ko Allah Ya sa su gano mana wanda ya aikata wa yarona haka.”

Babban Manajan Asibitin Namada da ke Azaran Dabowa kofar Gayan, Kamaliddin Nuhu ya ce sun yi masa duk abin da ya kamata a yi masa na kula kuma ya fara samun hakalinsa, sai dai idan suka kammala duba shi, za su tura shi asibitin ido domin a duba idanuwansa, saboda da alama sun dan samu matsala amma ba sosai ba, kuma suna sa ran zai iya samun sauki.

A lokacin da wakilinmu ya tuntubi ofishin ’yan sanda na Tudun Wada domin jin ta bakinsa, DPO mai kula da ofshin ya ce har zuwa lokacin bai samu rahoto mai kama da haka ba, amma idan bayani ya zo gare shi, zai yi iya kokarinsa ya dauki matakin da ya dace don gano wanda ya aikata hakan.