An wuce da Hama Amadou asibiti a Faransa

Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta fitar da dan takarar shugabancin a kasar karkashin jam’iyyar adawa Moden Lumana Hama Amadou, zuwa wani asibiti a kasar Faransa domin duba lafiyarsa.Kamar yaddda BBC ta bayyana an fara kai Amadou babban birnin kasar Niamey daga Filinge inda ake tsare da shi.An ruwaito cewa an kai shi ne a wani jirgin […]

An wuce da Hama Amadou asibiti a Faransa
An wuce da Hama Amadou asibiti a Faransa

Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta fitar da dan takarar shugabancin a kasar karkashin jam’iyyar adawa Moden Lumana Hama Amadou, zuwa wani asibiti a kasar Faransa domin duba lafiyarsa.
Kamar yaddda BBC ta bayyana an fara kai Amadou babban birnin kasar Niamey daga Filinge inda ake tsare da shi.
An ruwaito cewa an kai shi ne a wani jirgin sojojin Faransa, kuma daga nan aka wuce da shi birnin Paris domin duba lafiyarsa.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a san rashin lafiyar da ke damunsa ba.
Amadou na daga cikin ’yan takarar shugabancin kasar Nijar, amma tun a shekarar da ta gabata ne yake tsare a gidan yari saboda tuhumarsa da ake yi da safarar jarirai daga Najeriya.
Sai dai ya musanta zargin, yana mai cewa an yi hakan ne don a hana shi takarar shugabancin kasar.
A ranar Lahadi za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a jamhuriyyar Nijar.
Kuma a ranar Talatar da ta gabata ne aka tsare likitan Hama Amadou wato Yakubu Haruna, saboda nuna damuwarsa da ya yi kan lafiyar dan takarar.