An daure direba shekara 2 kan tukin ganganci
Kotun Majistare ta 21 da ke Nomanslands a Jihar Kano ta yanke wa wani direba mai suna Adamu Isma’ila mai kimanin shekara 32 daurin shekara biyu a kurkuku bisa samunsa da laifin tukin ganganci. Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Iliyasu Muhammad ya shaida wa kotun cewa wani dan sanda da ke ofishin ’yan […]
Kotun Majistare ta 21 da ke Nomanslands a Jihar Kano ta yanke wa wani direba mai suna Adamu Isma’ila mai kimanin shekara 32 daurin shekara biyu a kurkuku bisa samunsa da laifin tukin ganganci.
Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Iliyasu Muhammad ya shaida wa kotun cewa wani dan sanda da ke ofishin ’yan sanda na Fagge mai suna Lucky Gokir ya shigar da kara a kotun cewa wani direban motar tanka ta Kamfanim Man fetur na A. A. Rano mai suna Adamu Isma’ila ya haddasa aukuwar hadari a kan titin IBB kusa da babbar mayankar Kano, inda motar wani mai suna Sani Ahmad ta samu matsala.
Sai dai direban ya musanta laifin da ake zarginsa da shi na tuki ba tare da kula ba, wanda ya saba da sashe na 29 a cikin Kundin Shari’a na Final Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Halima Muhammad Nasir ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin shekara biyu a kurkuku ko biyan tarar Naira miliyan daya da dubu 805 da Naira 70.