An yaba wa mutanen da suka ba da kariya ga giwaye a Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yaba wa mutanen garin Ganten Fadama da ke karamar Hukumar Bagudo da Zariyar Kala-Kala a karamar Hukumar KoKo-Besse da ke jihar saboda kokarinsu na kare rayukan wasu giwaye uku da aka gani a dazukan garuruwan a kwanakin baya. Giwayen uku dai sun shigo dazukan garuruwan biyu ne […]

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yaba wa mutanen garin Ganten Fadama da ke karamar Hukumar Bagudo da Zariyar Kala-Kala a karamar Hukumar KoKo-Besse da ke jihar saboda kokarinsu na kare rayukan wasu giwaye uku da aka gani a dazukan garuruwan a kwanakin baya.
Giwayen uku dai sun shigo dazukan garuruwan biyu ne daga Jamhuriyyar Benin da ke da iyaka da jihar a karamar Hukumar Bagudo da Dandi.
Gwamna Bagudu ya yi wannan yabon ne yayin da yake gabatar da jawabin godiya ga jama’ar garuruwan da sauran jama’ar da suka taimaka wurin ganin cewa an kare rayuwar giwayen uku da suka shigo cikin jihar. “Makasudin ziyarar da na kawo shi ne, domin in gode wa mutanen Ganten Fadama da na Zariyar Kala-Kala saboda kokarinsu na ganin cewa sun kare lafiya da rayuwar giwayen da suka shigo jihar ta yankunansu, wadanda ake sa ran cewa sun zo ne daga Jamhuriyyar Benin a makon jiya,” inji Gwamnan.
Bugu da kari, Gwamnan ya gargadi jama’ar yankin Bagudo game da kashe dabbobin daji, musamman irin wadanan giwaye da suka shigo jihar, domin a cewarsa, dabbobin daji ne da ba kasafai ake ganinsu ba kuma dabbobi ne da aka haranta wa jama’a kashe su. Ya ce, “Jama’a kada a kashe su ko cutar da su, domin duk wanda ya cutar da su zai fuskanci hukunci mai tsanani.”
Wani wanda ya ga giwayen da idonsa mai suna dantallo Gante, ya shaida wa Aminiya cewa, “Na ga giwaye biyu suna kiwo a bakin gonar shinkafa mallakar Kamfanin Shinkafa na Labana a tsallaken Kogin Neja, wanda ya gitta a tsakani.”