An yaba wa Tambuwal da ya koma takarar Gwmanan Sakkwato
Alhaji Bara’u Rawaiya, wnai jigon jam’iyyar APC a Kalaba ya yi nuni da cewa dawuya jam’iyyar APC za ta kai labari matukar ta bai wa Honarabul Aminu Tambuwal bane ya tsaya mata takarar gwamna a zaben 2015. Ya ce gaba da kare hujjojinsa da cewa kakakin majalisar “mutum ne da kowa a jihar sa yake […]
Alhaji Bara’u Rawaiya, wnai jigon jam’iyyar APC a Kalaba ya yi nuni da cewa dawuya jam’iyyar APC za ta kai labari matukar ta bai wa Honarabul Aminu Tambuwal bane ya tsaya mata takarar gwamna a zaben 2015.
Ya ce gaba da kare hujjojinsa da cewa kakakin majalisar “mutum ne da kowa a jihar sa yake kawazucinsa, kuma yake sonsa da ya zama Gwamnan Jihar Sakkwato kuma yana da jama’a duk inda ya je ana nuna masa kauna idan musamman ma da ya janye takarar shugaban kasa.
“ APC kaf in banda Alu babu mai iya kayar da PDP sai shi ne kadai zai iya kawo kujerar ya kayar da jam’iyyar adawar jihar wato PDP.” Inji Rawaiya.
Mukamin Gwamnan Jihar Sakkwato ce ta fi dacewa da shugaban majalisar wakilai Honarabul, Aminu Waziri Tambuwal ba neman shugabancin kasa ba, a cewar Alhaji AbdusSalam Bara’u Rawaiya, wanda matashin dan siyasa ne a Kalaba.
Ya ce shi ma zai yi takarar shugaban kasa a maimakon ya tsaya a kara wa jam’iyya karfi da tagomashi a Jihar sakkwato yace ya fito takarar shugabancin kasa a APC”.
dan siyasar ya ce: “Ya yi daidai da ya koma neman takarar mukamin Gwamnan Jihar Sakkwa, don shi ya fi dacewa da Lallai ya kara matsa kaimin, don kada ya bar jama’a ciki8n tunani.”
Da yake tsokaci dangane da ragowar wadanda suka fito takarar mukamin shugabancin kasa a jamiyyar APC .Alhaji AbdusSalam Bara’u Rawaiya, ya ci gaba da cewa: “Kamata ya yi su hadu, su hada kan su su barwa mutum daya tun ma kafin a zo yin zaben fitar da gwani.”
A tasa fahimtar yana ganin abin da ya fi dacewa jam’iyya ta yi shi ne ta fitar da mutum daya tilo daga cikin duk wadanda suka nuna sha’awar takarar nan, a ba shi fom in ya so saura su nemi magoya bayan su da su kan su, su mara masa baya.
Daya juya kan ragowar yan takarar cewa ya yi “dukkan su su hakura su janye su barwa Gwamnan Kano injiniya Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, shi ya fi cancanta domin ba shi da tsoro jarumi ne, duniya ma ta shaida irin aikin da yake yi wa jiharsa “.
karshe ya yi fatan dukkan ’yan takara da uwar jam’iyyar za su zauna teburin shawara su yi tunanin wanda zai fi cancanta su tsayar da shi ya yi takara da sauran abokan hamayya.