An yanke hukuncin kisa ga ’yan Ikhwanu 528 kan kashe dan sanda
Babbar Kotun Minya da ke kasar Masar ta yanke hukuncin kisa ga magoya bayan hambararren Shugaban kasar Mohammad Morsi 528, ciki har da shugabannin kungiyar ’yan uwa Musulmi, kan laifin kashe dan sanda daya a yayin da suke zanga-zanga.Hukuncin ya shafi mutum 150 da ke tsare da wadanda aka yanke wa hukunci a bayansu, kuma […]
Babbar Kotun Minya da ke kasar Masar ta yanke hukuncin kisa ga magoya bayan hambararren Shugaban kasar Mohammad Morsi 528, ciki har da shugabannin kungiyar ’yan uwa Musulmi, kan laifin kashe dan sanda daya a yayin da suke zanga-zanga.
Hukuncin ya shafi mutum 150 da ke tsare da wadanda aka yanke wa hukunci a bayansu, kuma kotun ta wanke mutum16.
An samu mutum 528 da hannu a laifin kisan wani dan sanda tare da far wa ’yan sanda, a lokacin zaman dirshan na nuna goyon baya ga hambararren shugaban, a daidai lokacin da jami’an tsaro ke kokarin tarwatsa zaman dirshan din da suka yi, wadda ‘’yan sanda suka tarwatsa a watan Agustan shekarar 2013 da karfin tuwo.
Lauyoyin da ke kare mutanen sun ce, ba a ba su damar kare wadanda aka yanke wa hukuncin yadda ya kamata ba, kuma ana sa ran za su daukaka kara.
A ranar Talata wato bayan kwana daya da yanke wannan hukunci wata kotu a Masar ta fara shari’ar wasu ’yan kungiyar Ikhwanu 682, ciki har da shugaban kungiyar Mohammed Badie.
Sai dai Malam Badie bai halarci zaman kotun ba, saboda abin da hukumomi suka kira dalilai na tsaro.
Amma wadanda ake zargin 60 ne suka halarci zaman kotun, sauran ana yin shari’ar ne a bayan idonsu.
Badie da sauran mutanen za su fuskanci tuhuma game da tunzura mutane su yi tashin hankali da kisan wasu masu bore domin adawa da kungiyar Ikhwanu su takwas, a kofar hedkwatar kungiyar a Alkhahira.
Majalisar dinkin Duniya ta yi Allah wadai da yanke hukuncin kisan ta bakin Kwamishinan Kare ’Yancin dan Adam ta Majalisar Nabi Pillay. Wani kakakin Pillay ya ce shari’ar dimbin jama’a a lokaci guda cike take da rashin bin ka’ida tare da keta dokokin kare hakkin dan Adam na duniya.