An yanke wa Abdul Nyass hukuncin kisa
Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke wa malamin nan mai suna Abdul’aziz Dauda wanda aka fi sani da Abdul Nyass hukuncin kisa bisa samunsa da laifin yin kalaman batanci ga Annabi (SAW).A takardar karar da aka gabatar wa kotun an bayyana cewa a ranar 13 ga watan Mayun bara ne malamin […]
Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke wa malamin nan mai suna Abdul’aziz Dauda wanda aka fi sani da Abdul Nyass hukuncin kisa bisa samunsa da laifin yin kalaman batanci ga Annabi (SAW).
A takardar karar da aka gabatar wa kotun an bayyana cewa a ranar 13 ga watan Mayun bara ne malamin ya yi kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a wajen taron Mauludin Nyass da ya yi a Kano lamarin da ya yi sanadiyar tayar da hankulan jama’a har ya janyo aka kone kotun farko da aka yi niyyar gabatar da shi a gabanta a Rijiyar Lemo da ke birnin Kano.
Gwamnatin Jihar Kano ce ta yi karar malamin tana zarginsa da laifuffuka biyu da suka hada da kalaman batanci ga Annabi (SAW) da kuma na tayar da hankulan jama’a wadanda suka saba wa sashi na 275 na Kundin Shari’ar Musulunci na Jihar shekarar 2000.
Da yake yanke hukunci a kan karar, Alkalin Kotun Mai shari’a Muhammad Atiku ya bayyana cewa za a zartar wa mai laifin hukuncin kisa ne ta hanyar rataya.
Baya ga hukuncin kisan Alkalin ya yanke masa hukuncin daurin shekara uku bisa samunsa da laifin tayar
da hankalin jama’a.
Alkalin ya ce mai laifin yana da damar daukaka kara cikin kwanaki 30 daga ranar yanke hukuncin.
Lauyan Gwamnati Barista Lamido Abba Soron dinki ya bayyana wa Aminiya cewa mai laifin ya amsa laifuffukan da ake zarginsa a wani zama da kotun ta yi, kuma ya ce za su ci gaba da bibiyar shari’ar idan har mai laifin ya daukaka kara.
Jami’an tsaro sun tafi da wanda ake zargin Abuja bayan zartar da hukuncin wanda aka gudanar cikin tsauraran matakan tsaro.