An yanke wa barayin waya hukuncin rataya
Wasu matasa biyu za su fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kwacen waya
Wasu matasa biyu masu shekaru 25 da 32 za su fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kama su da laifin satar waya da na’urar power Bank a Jihar Ekiti.
Wata babbar kotun jihar da ke zamanta a Ado Ekiti ce ta yanke hukuncin bayan samun su da laifin fashi da makami.
An gurfanar da mutanen biyu ne a gaban Mai Shari’a Blessing Ajileye a ranar 30 ga watan Disamba, 2022, bisa zargin hada baki, fashi da makami da kuma mallakar makamai.
Kotun ta gano cewa a ranar 16 ga Agusta, 2022, a kan titin Iluomoba, matasan suka hada baki wajen yin fashi da makami.
- Kotu ta dakatar da rushe masarautun Kano
- NAJERIYA A YAU: Abu Na Gaba Da Zai Faru Da Sarakunan Kano Da Aka Tuɓe
An kama su da bindigogi da wukake da adduna, sun kuma yi wa wasu mutane biyu fashin waya da power bank da katin ATM da tsabar kudi N105,000 daga wurin wasu mutane biyu.
Mai gabatar da kara ya zo da shaidu shida kuma duk sun tabbatar da faruwar lamarin.
Wadanda ake tuhumar, da lauyansu Adeyinka Opaleke ya wakilta, ya nemi kare su amma ba su kawo shaidu ba.
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’a Blessing Ajileye ta ce, “Na gano cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da cewa an yi fashi da makami a ranar 16 ga Agusta, 2022.
“Saboda haka hukuncin da kotun ta yanke shi ne a rataye su a wuya har sai sun mutu. Allah ya jikan ku da rahama.”