An yanke wa dan bindiga hukuncin bindigewa
Kotu ta kama direban ’yan bindiga da laifin hada baki da kuma satar mutane.
Wata Babbar Kotun Jiha da ke zamanta a garin Yenagoa a Jihar Bayelsa, ta yanke wa wani mai garkuwa da mutane hukuncin kisa ta hanyar harbewa.
Wanda aka yanke wa hukucin mai shekara 39, kotun ta same shi da laifin yin garkuwa da matar wani fitaccen dan kasuwa a jihar, Vivian Okoye da wani likita mai suna Alex Ogregade Ileimokumo.
- Kifi ya hadiye dan ninkaya ya amayar da shi da rai
- Za a rataye ’yan bindiga da masu satar mutane a Neja
Gungun ’yan bindigar sun yi yunkurin garkuwa da Vivian, wadda ita ce ke da manyan shagunan sayar da kayan wutar lantarki na A-Z a sassan garin Yenagoa da likitan ne a yankin Igbedi na Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu da Jihar.
Sai dai kuma masu garkuwar ba su nasara ba, inda ’yan sandan rundunar ‘Operation Puff Adder’ a Jihar suka ceto mutanen biyu bayan dauki-ba-dadi da suka yi da ’yan bindigar da suka sace su.
Dan bindigar, wanda kuma shi ne direban gungun ’yan bindigar da suka yi yunkurin garkuwa da mutanen, an gurfanar da shi a gaban kotun ne, bisa tuhumar sa da hada baki da kuma yin garkuwa da mutane.