An yanke wa dattijo lafiyayyar kafa aka bar mai ciwon
Wani asibiti ya yi azarbabin yanke lafiyayyar kafar dattijo mai shekara 82.
Wani asibiti a Austria ya yi azarbabin yanke lafiyayyar kafar marar lafiya.
Asibitin da ke garin Freistadt ya dora laifin yanke kafar dattijon a kan kuskuren dan Adam kuma ‘gagarumin kuskure’.
Mara lafiyan na fama ne da cututtuka daban-daban, amma ya fi fama da wadanda suka shafi kafufunsa, har ta kai ga dole a yanke kafarsa ta hagu.
“Mun kadu sosai, duk da tabbacin ingancin aikinmu, mun yanke kafar da ba ta da ciwo ta wani tsoho mai shekara 82…,” inji asibitin, yana mai cewa an gano kuskuren ne lokacin da ake sauya wa marar lafiyan bandeji kwana biyu bayan aikin.
Kuskuren ya faru ne jim kadan gabanin fara aikin, lokacin da ake sanya wa kafar da za a yanken alama, inji asibitin.
“Abin takaici ya faru inda aka yanke kafar dama maimakon kafar hagu bisa wasu kurakurai da suka yi ta faruwa,” a cewar asibitin.
Ya kara da cewa ana nan ana gudanar da binciken ainihin abin da ya haifar da gagarumin kuskuren.
An rarrashi tsohon, kuma lallai ne a sake masa aikin cire kafarsa ta hagun daga tsakiyar cinyarsa.
“Nan gaba kadan za a yi aikin,” inji asibitin.