An yanke wa karamar yarinya al’aura a Bauchi
Gwamnati ta sa a kamo bokaye a kuma rusa matattarar bata-gari
Shugaban Karamar Hukumar Jama’are a Jihar Bauchi, Samaila Jarma, ya ba da umarni rushe wata matattarar bata-gari da ta yi kaurin suna a yankin nan take.
Ya bayar da umarnin ne bayan wasu batag-gari sun yanke al’aurar wa wata karamar yarinya mai shekara shida a garin na Jama’are.
Ya kuma bayar da umari cafke dun wani baoka da aka san yana tsubbace-tsubbace musamman wa matasa aikin yi.
- Rage albashi a Kano ya tayar da kura
- Miji ya tsere bayan Matarsa ta haifi ’Yan hudu
- Sarakuna ke gayyato ’yan bingida —Gwamnan Neja
- Rikicin zabe: An gano bama-bamai, mutum 4 sun mutu a Majalisar Amurka
Jarma ya ce daukar matakin ya zama tilas somin taka wa masu aikata migayun ayyuka a yankin burki ciki har da masu tsafin neman kudi.
Ya ce Karamar Hukumar ta ba wa jami’an tsaro umarnin kamawa da kuma gurfanar da duk wanda ke da alaka da miyagun ayyuka a yankin musamnan masu kai wa raunana farmaki.
Jarma ya kuma yi watsi da wani sakon nema wa karamar yarinyar taimako da ke ta yawo a kafafen sada zumunta.
“Gwamna Bala Mohammed ya dauki nauyin kula da lafiyarta.Gwamnati ta riga ta bayar da Naira miliyan daya domin a fara mata aiki.
“Za a faitar da karin kudi gwargwadon bukata ga kwararrun lafiya da ke kula da ita.
“A matsayinmu na Karamar Hukuma, mun isar wa iyalantsa kayan abinci da sauran bukatu, kuma za mu ci gaba da taimakawa,” inji.