An yanke wa Lauyar da ta kashe mijinta hukuncin daurin shekara bakwai

Wata kotun Jihar Oyo a birnin Ibadan Jiya ta yankema wata Lauya mace , Yewande Oyediran hukuncin shekara bakwai a gidan yari. An kamata da laifin soka wa mijinta wuka da ya aika sa lahira. Alkalin, Munta Abimbola yace kotun ta kamata da kisan kai na kuskure ba kisan kai da aka tuhumeta dashi ba. […]

An yanke wa Lauyar da ta kashe mijinta hukuncin daurin shekara bakwai

Wata kotun Jihar Oyo a birnin Ibadan Jiya ta yankema wata Lauya mace , Yewande Oyediran hukuncin shekara bakwai a gidan yari. An kamata da laifin soka wa mijinta wuka da ya aika sa lahira.

Alkalin, Munta Abimbola yace kotun ta kamata da kisan kai na kuskure ba kisan kai da aka tuhumeta dashi ba.

Abimbola yace dukda masu tuhuma sun tabbatar da cewa ita ta kashe marigayin, sun kasa tabbatar da cewa da gangan tayi.

Alkalin ya bada umurni cewa shekara bakwai din za a fara irgenshi ne daga 2 ga watan Fabrairu, 2016, lokacin da aka kamata.

Ya ce, Shaidun  da aka kawo kotu sun nuna cewa wadda aka kama da mijinta suna yawan rikici a tsakaninsu.

Yayi hukunci da shaidar da mai masauki da matarsa Akinpelu suka bayar a matsayin sahihi.

Mai masaukin da matarsa sun ce sunga mai laifin da wuka a hannunta a lokacin da marigayin yake male-male kwance cikin jini.

“Ganin wadda ake tuhuma rike da wuka a hannunta, kuma ta fadi cewa ta soka masa almakashi ana I gobe, na rika cewa ita ce ta soki marigayin”

Abimbola ya ce ya yi amfani da  bincike musababbin mutuwa da ake yi wa lakabi da “autopsy” da Farfesa Abideen Oluwashola, mai bada shawara na Asibitin hortar da likitoci da ke Jami’ar Ibadan, wanda ya nuna cewa marigayin ya mutu ne saboda rudani daga ciwo mai zurfi na abu mai kaifi.

Kotun ta ce ba za ta iya amfani da bayanin mai laifin ba, tunda abin da ta fada wa ‘yan sanda daban yake da abin da ta fada a kotu.

Oyediran Ma’aikaciyar hukumar DPP a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Oyo ta kashe mijinta, ta hanyar soka masa wuka a ranar biyu ga watan Fabrairu 2016 a yankin Akobo na Birnin Ibadan. (Kamfanin dillacin labaru na Najeriya)

 “Hukumcin daurin shekaru 7 a gidan yari da babbar kotun Jihar Oyo ta yanke wa Lauya Yewande ya yi kadan ga irin wannan mata da tayi sanadin mutuwar mijinta ta hanyar daba masa wuka a wuyansa. Ya kamata gwamnatocin jihohin da gwamnatin tarayya su sake yin gyara a cikin kundin tsarin shari’ar kisan kai, ta yadda za a rinka yanke hukumci mai tsanani ga wanda aka samu da laifin kisan kai da gangan.”

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Ustaz Tahir Zubairu cikin hira da Aminiya jim kadan bayan babbar kotun Jihar Oyo ta yanke wa Yewande hukumcin daurin shekaru 7 a gidan yari bayan samunta da laifin daba wa mijin ta mai suna Oyelowo Oyediran, wuka a wuyansa da ya yi sanadin mutuwarsa. Malamin ya ce, “hukumci mai tsanani ne zai iya zama darasi ga irin wadannan mata.”

Wani bakanike a Ibadan mai suna Sulaiman Abdu cewa ya yi, “a gaskiya ban gamsu da wannan hukumci ba. Kamata ya yi a yanke mata hukumcin kisa ta hanyar ratayewa. Wannan hukunci bai yi ba ko kadan, domin alama ce da ke nuna cewa kotun ta yanke mata hukumci mai sauki ne saboda ‘yar manyan mutane ce.”

A ranar litinin da ta gabata ne Alkalin babbar kotun Jihar Oyo, Maim Shari’a Munta Abimbola ya zartar da hukumcin shekaru 7 ga  Yewande mai shekaru 29 wacce lauya ce da ke aiki a ma’aikatar shari’a ta Jihar oyo da kotun ta tuhume ta da laifin kashe mijinta Oyelowo mai shekaru 38 ta hanyar daba masa wuka a wuya.

Takardar tuhuma da aka karantawa Yewande a cikin kotun, ta nuna cewa, a ranar 2 ga watan Fabrairu na shekara ta 2016 da misalin karfe 6 da minti 10 na safe ne ta aikata laifin da ake tuhumarta ta hanyar daba wa mijinta wuka da ya yi sanadin mutuwarsa. Bayanin tuhumar ya nuna cewa wannan mata ta aikata laifin ne a cikin gidan da suke zaune tare da mijinta a unguwar Akobo a birnin Ibadan.

Duk da yake Lauya Yewande ba ta amsa laifin da aka tuhume ta da aikatawa ba sai dai, Alkalin ya ce ya yanke wannan hukumci ne saboda rokon da lauyoyi masu kariya suka yi ne da suka nemi a yi mata sauki wajen yanke mata hukumci. Kotun ta ce Yewande ta ki yin aiki da matsayinta na lauya a lokacin da irin wannan al’amari ya fara aukuwa a tsakaninta da mijinta wanda ya yi sanadin garzayawa da mijinta zuwa asibiti saboda raunin da ta yi masa. Kotun ta ce ya kamata ta yi aiki da matsayinta na lauya kafin ta sake aikata danyen aikin a karo na biyu da ya yi sanadin mutuwar mijin nata.