An yanke wa mai nufin yi wa ’ya’yansa fyade ya cinye su daurin shekara 27
An yanke hukuncin shekara 27 na zamanin kurkuku ga wani mutumin Birtaniya da ke zaune a Amurka, wanda aka samu da laifinhada kai da wasu mutane kan yadda za su rika sace kananan yara, su yi musu fyade, su halaka su, sannan su cinye su. An kuma same shi da kokarin sace ’ya’yansa, ya yi […]
An yanke hukuncin shekara 27 na zamanin kurkuku ga wani mutumin Birtaniya da ke zaune a Amurka, wanda aka samu da laifinhada kai da wasu mutane kan yadda za su rika sace kananan yara, su yi musu fyade, su halaka su, sannan su cinye su. An kuma same shi da kokarin sace ’ya’yansa, ya yi musu fyade, sannan ya halaka su.
Mutumin mai suna Geoffrey Portway, dan shekara 40 na daya daga cikin mutum 60 da aka kama, bayan an gudanar da binciken masu shirya hotunan batsa da lalata da kananan yara a fadin duniya, wanda aka yi a birnin Massachusettts, al’amarin da ya karade kasashe 12. Wani lauya a kasar Amurka, Stacy Dawson Belf ya bayyana cewa akalla yara 167 suka fada hannun wadannan miyagun mutane, amma an ceto su.
Portway, mutum ne mai yawo a duniya, don bai cika zama a wuri guda. Don haka a matsayinsa na dan Birtaniya, Kotun Gunduma ta Amurka ta bayar da umarnin a kai shi kasarsa ta haihuwa ya yi zaman kurkukunsa a can, kamar yadda alkali Timothy Hillman ya yanke hukunci.
Alkali Belf dai ya karya kariyar da lauyan Portwsay ya yin a cewa wai barkwanci ne kawai yake yi, don haka ya nemi taimakon mutanen da za su hada karfi wajen satar yara, su kashe su.