An yanke wa mai sayar da tikitin keke Napep hukuncin kisa

Kotun ta kuma yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai kan yunƙurin kisan kai da kuma shekara 14 a gidan yari

An yanke wa mai sayar da tikitin keke Napep hukuncin kisa

Rataya

Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom, da ke Ikot Ekpene ta yanke wa wani mai sayar da tikitin Keke NAPEP ko adaidaita sahu, Iboro Sunday Akpan hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin fashi da makami.

Kotun ta kuma yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai kan yunƙurin kisan kai da kuma shekara 14 a gidan yari kan haɗa baki wajen aikata laifin.

An same shi da laifin kai hari tare da wasu mutane a wani gida da ke Ikot Ekpene a watan Yulin 2025, inda suka sace kuɗi da kayan ado tare da harbin wani mutum.

Mai Shari’a Augustine Odokwo ya ce, hujjojin da masu gabatar da ƙara suka gabatar sun tabbatar da laifin wanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba.

Kotun ta yi watsi da iƙirarin da Akpan ya yi na cewa, ba ya wurin da aka aikata laifin tana mai cewa wanda aka kai wa harin ya san shi tun kafin aukuwar lamarin.

Daga ƙarshe, kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin fashi da makami.