An yanke wa malama daurin shekara 600 saboda lalata da dalibi

A wancan lokaci malamar tana da shekara 67 shi kuma dalibin yana dan shekara 14.

An yanke wa malama daurin shekara 600 saboda lalata da dalibi

Wata malamar makaranta da ake kira Misis Anne N.Koch mai shekara 74 a duniya, za ta karasa rayuwarta a gidan yari bayan da aka yanke mata hukuncin daurin shekara 600 saboda samun ta da aikata lalata da wani yaro a wata makaranta mai zaman kanta da ke Wisconsin na Kasar Amurka.

An tuhumi Nelson-Koch da laifuffuka 25 bayan wani hari da aka kai wa makarantar a tsakanin shekara 2016 da 2017.

Al-Manasik Reporters ta ruwaito cewa tsohuwar malamar na daukar yaron zuwa wani wuri a cikin makarantar wacce aka sakaya sunanta, domin ta yi lalata da shi.

A wancan lokaci Misis Nelson-Koch tana da  shekara 67 shi kuma dalibin yana dan shekara 14.

An yanke wa wannan tsohuwa hukunci ne a Kotun Monroe County bayan daukar tsawon awa biyar ana nazartar shari’ar.

Mai gabatar da kara ta ce, Misis Nelson Koch za ta ci gaba da zama a hannun jami’an tsaro kafin zuwa ranar 27 ga Oktoba da za a zartar da wannan hukunci.

Sai dai Mai shari’a Mista Richard Radcliffe ya bayar da belinta, tare da sharadin za ta rika yin amfani da na’urar da ke nuna wurin da mutum yake (GPS) har zuwa ranar da za a sake sauraron shari’ar.

Babban Alkalin Kotun Gundumar Monroe County, Mai shari’a Kevin Croninger ya ce, malamar za ta iya shafe sama da shekara 600 a gidan kurkuku.

Mataimakiyar Babban Alqalin Mai shari’a Sarah Skiles wadda ita ce mai gabatar da kara, ta ce: “Abin takaicin wanda aka aikatawa wannan laifi yaro ne karami.

“Ya fadi gaskiya, kuma masu yanke hukunci sun ji bayanansa sosai. Muna godiya ga alkalan da suka sadaukar da lokutansu har suka gano gaskiya,” in ji ta.

Skiles ta yaba wa Paul Sloan na caji ofis ’yan sandan Thomas wanda shi ne dan sandan da ya jagoranci binciken.

“Ba za a taba samun wannan nasarar ba, in ba don wadannan jami’ai sun nuna jarumta da sadaukarwa wajen gudanar da bincike ba.

“Haka shi ma dan sandan ya yi matukar kokari wajen taimakawa a gabatar da wannan mai laifi a gaban kotu.”

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra