An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna

Kotu ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin ratayewa da kuma dandaƙewa kan laifin aikata fyaɗe a Jihar Kaduna.

An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna

(Hoto: us.fotolia.com)

An yanke wa wasu mutum uku da aka kama da laifin fyaɗe hukuncin ratayewa da kuma dandaƙewa a Jihar Kaduna.

Kwamishinar Kula da Walwalar Jama”a, Hajiya Rabi Salisu, ta bayyana fatan cewa hukuncin da kotu ta yanke wa masu laifin zai zama darasi ga masu muguwar ɗabi’ar ta fyaɗe.

Da take sanar da hakan a ranar Laraba, kwamishinar ta bayyana cewa Ma’aikatar ta yi nasara a Shari’o’i uku da ta shigar da ƙara kan masu aikata fyaɗe a shekara gudanar ta gabata.

Ta bayyana cewa daga cikin mutanen akwai wanda Mai Shari’a Nana ta Babbar Kotun jihar ta yanke masa da hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya, a watan Yuni shekarar 2024.

“Ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025 kuma Mai Shari’a B. Yusuf na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya yanke wa na biyun hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya kan laifin fyaɗe.

“A ranar 24 ga watan kuma Mai Shari’a Isa Aliyu in yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai fa wanda wanda aka samu da laifin.”