An yanke wa Shugaban Jam’iyyar Musulmi hukuncin kisa a Bangaladesh

Wata kotun musamman a kasar Bangladesh ta yanke wa shugaban Jam’iyyar Jama’atul Islam Moti’ur Rahman Nizami hukuncin kisa bayan ta tuhume shi da aikata laifuffukan yaki a lokacin gwagwarmayar kwatar ’yancin kasar daga kasar Pakistan a 1971. Kotun ta samu Moti’ur Rahman Nizami da aikata laifuffuka 71 da suka hada da kisan kai da fyade […]

An yanke wa Shugaban Jam’iyyar Musulmi hukuncin kisa a Bangaladesh
An yanke wa Shugaban Jam’iyyar Musulmi hukuncin kisa a Bangaladesh

Wata kotun musamman a kasar Bangladesh ta yanke wa shugaban Jam’iyyar Jama’atul Islam Moti’ur Rahman Nizami hukuncin kisa bayan ta tuhume shi da aikata laifuffukan yaki a lokacin gwagwarmayar kwatar ’yancin kasar daga kasar Pakistan a 1971.

Kotun ta samu Moti’ur Rahman Nizami da aikata laifuffuka 71 da suka hada da kisan kai da fyade da wawurar dukiyoyin jama’a lokacin yakin neman ’yancin.
Babban alkalin kotun, Enayetur Rahim ya yanke hukuncin a rataye Nizami a wuya har sai ya mutu saboda shirya kashe likitoci da masana da sauransu a lokacin da ya jagoranci wata kungiyar mayaka masu dauke da makamai.
Tuni dai hukumomin kasar Bangladesh suka tsaurara matakan tsaro a cikin kasar saboda tsoron barkewar rikici daga magoya bayan Jam’iyyar Jama’atul Islam wadda ita ce babbar Jam’iyyar Musulunci a kasar mai rinjayen Musulmi idan aka yanke hukunci irin wannan hukunci na kisa.
Irin wannan hukunci ne aka yanke wa wasu mataimakan Sheikh Nizami inda suka haifar da tashin hankali a kasar wanda ya yi sanadin kashe mutane sama da 500.
Ministan Harkokin Cikin gidan kasar, Asaduzzaman Khan ya ce sun dauki dukkan matakan da suka dace don dakile duk wani tashin hankali da ka iya biyo bayan yanke hukuncin a kasar.