An yanke wa tsohon dan tseren Najeriya hukuncin rai-da-rai a Afirka ta Kudu

An yanke wa tsohon dan tseren Najeriya mai suna Monye Ambrose hukuncin rai-da-rai a Afirka ta Kudu bayan wata kotu ta same shi da laifin hada baki wajen kashe wata mata ’yar kimanin shekara 26 mai suna Channelle Henning.Tsohon dan tseren, ya wakilci Najeriya a gasar wasanni ta Olamfik da ta gudana a shekarar 1988.  […]

An yanke wa tsohon dan tseren Najeriya hukuncin rai-da-rai a Afirka ta Kudu

An yanke wa tsohon dan tseren Najeriya mai suna Monye Ambrose hukuncin rai-da-rai a Afirka ta Kudu bayan wata kotu ta same shi da laifin hada baki wajen kashe wata mata ’yar kimanin shekara 26 mai suna Channelle Henning.
Tsohon dan tseren, ya wakilci Najeriya a gasar wasanni ta Olamfik da ta gudana a shekarar 1988.  An same shi da laifin kashe matar ce ta hanyar yi mata kwanton-bauna a cikin motarta jim kadan bayan ta ajiye danta a wata makaranta mai suna Morning Star Montoessori Perschool da ke yankin Faere Glen a Gabashin Pretoria da ke Afirka ta Kudu.  Al’amarin kisan ya faru ne a ranar 8 ga watan Nuwamban, 2011.
Kamar yadda wani rahoto ya nuna, Monye tare da abokinsa Andre Gouws da shi ma aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai an same su da laifin hada baki wajen kashe matar ce bayan mijin matar ya dauke su a matsayin sojojin-haya bayan ya biya su maqudan kudi..
Da farko sun shaidawa kotu ba su da hannu a laifin da ake zargiunsu bayan an shafe kusan shekara biyu ana shari’ar amma sun amsa laifinsu ne a qarshen makon jiya a iqirarin da suka yi da kansu na cewa suna da hannu a laifin kisan kan.
Andre Gouws, daya daga cikin wadanda aka samu da laifin ya shaida wa kotu cewa mijin matar mai suna Nick da suka dade suna taqaddama da matarsa Channelle a kan wanda ke da ikon mallaka dan nasu ne ya dauke su a matsayin sojojin-haya don ganin sun kashe matar tasa don ya samu damar mallakar dan nasu.  Ya ce hakan ta sa mijin ya tuntube shi a kan ya kashe Channelle bayan ya yi masa alqawarin Rand miliyan daya.
Ya qara da cewa bayan ya amince da kwangilar ne shi kuma ya tuntubi Monye Ambrose (dan Najeriya) a kan zai ba shi Ran dubu 500.  Daga nan ne suka sake daukar hayar wadansu mutum biyu masu suna  Gehardus (Doepie) du Please da Wilem (Tattoo) wadanda suka aiwatar da kisan ta hanyar harbeta da bindiga a motar ta jim kadan bayan ta ajiye danta a makaranta.
Shi dai dan Najeriya Monye ya yi qaurin suna a tarihin kashe mutane a Afirka ta Kudu. A shekarar 2011 ma jami’an tsaro sun taba kama shi a bisa zargin kashe wani ta hanyar lakada masa duka har rai ya yi halinsa amma daga bisani kotu ta bayar da belinsa.
Ambrose ya mallaki kamfanin horar da masu gadi ne (Security ) a Afirka ta Kudu a matsayin hanyar samun kudin shigarsa.