An yanke wa tsohon Shugaban Afirka ta Kudu hukuncin wata 15 a gidan yari

An yanke masa hukuncin ne saboda gaza bayyana a gaban wani kwamitin bincike.

An yanke wa tsohon Shugaban Afirka ta Kudu hukuncin wata 15 a gidan yari

Kotun Kundin Tsarin Mulki ta Afirka ta Kudu ta yanke wa tsohon Shugaban kasar, Jacob Zuma hukuncin wata 15 a gidan yari saboda raina kotu.

Hukuncin na zuwa ne bayan tsohon Shugaban ya gaza bayyana a gaban wani kwamiti don amsa zarge-zargen da ake masa da suka shafi cin hanci da rashawa a farkon wannan shekarar.

Jacob Zuma dai ya gaza bayyana a gaban Kwamitin Bincike ne da ke karkashin jagorancin Mataimakin Alkalin-alkalan kasar, Raymond Zondo a watan Fabrairu, lamarin da ya sa lauyoyi suka garzaya gaban kotun suna neman a daure shi.

Kwamitin dai na binciken zarge-zargen rashawa ne lokacin mulkin Zuma tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018.

Sai dai ya sha karyata dukkan zarge-zargen a baya, tare da kin bayar da hadin kai a binciken da ake masa.

“Za a aike da Mista Jacob Zuma gidan yari har tsawon wata 15,” inji Alkalin kotun lokacin da yake karanto hukuncin.

Alkalin ya kuma ce Tsohon shugaban na da kwanaki biyar domin ya bayyana a gaban ’yan sanda.

Kakakin tsohon Shugaban ya shaida wa gidan talabijin na eNCA cewa Mista Zuma zai fitar da sanarwar nan ba da jimawa ba.

Zarge-zargen da ake yi wa tsohon Shugaban dai sun hada da barin dan kasuwar da ke da kusanci da shi, Atul Ajay Rajesh Gupta, da yin facaka da dukiyar kasar.

Daga bisani dai wanda ake zargin ya tsallake ya bar kasar bayan saukar Mista Zuma daga mulki, a kokarin kaucewa titsiyen wanda ya gaje shi, Cyril Ramaphosa.

Ramaphosa dai na kokarin dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari zuwa kasar, duk da adawar da yake fuskanta daga tsagin jam’iyyar ANC da har yanzu ke biyayya ga Mista Zuma. (Reuters/NAN)