An yanke wa tsohon Shugaban Pakistan Perbez Musharraf hukuncin kisa
Kotun Pakistan ta yanke wa tsohon Shugaban mulkin sojin Kasar, Janar Perbez Musharraf hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin cin amanar kasa. Wani kusa a gwamnatin kasar Pakistan da ya tabbatar da wannan hukunci da kotun ta yi kan Musharaf, ya ce tsohon Shugaban ya aikata laifin da ya kai ga yanke masa […]
Kotun Pakistan ta yanke wa tsohon Shugaban mulkin sojin Kasar, Janar Perbez Musharraf hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin cin amanar kasa. Wani kusa a gwamnatin kasar Pakistan da ya tabbatar da wannan hukunci da kotun ta yi kan Musharaf, ya ce tsohon Shugaban ya aikata laifin da ya kai ga yanke masa hukuncin kisa ne bayan ya taka doka mai lamba ta shida ta kundin tsarin mulkin kasar.
Laifuffukan tsohon Shugaban sun hada da jingine tsarin mulkin kasar da kuma sanya dokar ta-baci a kasar a shekarar 2007.
Kotun ta musamman da ke birnin Islamabad ta yanke hukuncin kisan ne a bayan idon Musharraf da ke gudun hijira, yayin da lauyansa ke cewa, an tuhume shi ne saboda matakinsa na jingine Kundin Tsarin Mulkin Pakistan tare da amfani da kudiri na musamman a shekarar 2007. Tun a shekarar 2016 Janar Musharraf ke zaune a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa inda yake jinya don haka an yanke hukuncin ne yayin da yake wajen kasar. Tun daga wancan lokaci, Musharraf mai shekara 76 ya fi yin balaguro tsakanin Dubai da birnin Landan.
A 1999, Musharraf ya yi juyin mulki a Pakistan inda ya ci gaba da shugabancin kasar daga 2001 zuwa 2008 lokacin da ya yi murabus.
A watan jiya ne alkalai uku na kotun suka yanke hukuncin, amma Babbar Kotun Kasar ta hana su bayyana hukuncin.
An yi ta zanga-zangar adawa da gwamnatin Musharraf, lamarin da ya tilasta masa murabus a daidai lokacin da aka fara zaman sauraren bahasin tsige shi daga karagar mulki.
Lauyan Musharaf ya ce, a halin yanzu, tsohon Shugaban na fama da jinya a Dubai, inda ya kara da cewa, kawo yanzu, ba su tsayar da shawarar daukaka kara ba domin kalubalantar hukuncin kisan.
Musharraf wanda aka haifa a 1943 a birnin New Delhi na India, ya dare kan karagar mulkin Pakistan bayan ya jagoranci kifar da gwamnatin Firayi Minista Nawaz Sharif a wani juyin mulkin da ba a zubar da jini ba a 1999.