An yanke wa tsohuwar Shugabar Thailand daurin shekara 5

An samu tsohuwar Firayi Ministan Thailand, Misis Yingluck Shinawatra da laifin sakaci inda aka daure ta shekara biyar duk da ta gudu daga kasarta. Kotun koli ta kasar ce ta yanke mata wannan hukunci kan yadda ta tafiyar da harkar tallafin shinkafa da ake jin ta jawo wa kasar asarar Dala biliyan 8 (kimanin Naira […]

An yanke wa tsohuwar Shugabar Thailand daurin shekara 5

An samu tsohuwar Firayi Ministan Thailand, Misis Yingluck Shinawatra da laifin sakaci inda aka daure ta shekara biyar duk da ta gudu daga kasarta.

Kotun koli ta kasar ce ta yanke mata wannan hukunci kan yadda ta tafiyar da harkar tallafin shinkafa da ake jin ta jawo wa kasar asarar Dala biliyan 8 (kimanin Naira tiriliyan biyu da miliyan 928).

An cire ta daga shugabancin kasar a shekarar 2014, ’yan makonni kafin wani juyin mulkin soja kuma daga baya majalisa ta tsige ta daga mulki, sai dai Misis Yingluck ta musanta dukan zarge-zargen da ake yi mata inda ta gudu daga kasar kafin a yanke mata hukunci kuma rahotanni sun ce tana gudu Dubai.

A lokacin da ake yi mata shari’a, Misis Yingluck ta ce ba ita ce ke da alhakin gudanar da shirin yau da kullum ba, inda ta nace cewa ana yi mata bi-ta-da-kullin siyasa ce.

Shirin bayar da tallafin shinkafar dai yana cikin alkawuran da Misis Yingluck ta yi a lokacin kamfe, kuma ta kaddamar da shi a shekarar 2011 domin magance talauci a yankunan karkara, inda gwamnati take biyan manoman karkara ninki biyu na kudin da ake sayar da shinkafar a kasuwa.

Shirin ya kawo koma-baya ga fitar da shinkafa daga kasar Thailand inda gwamnatin sojin kasar ta ce ya jawo asarar akalla Dala biliyan takwas.

Kuma duk da cewa masu jefa kuri’a a yankunan karkara suna goyon bayanta,abokan adawa sun ce shirin ya yi muguwar tsada tare buda kafar almundahana.

Rahotanni sun ce Misis Yingluck tana Dubai inda dan uwanta tsohon Firayi Ministan kasar Thaksin Shinawatra, ke zaman gudun hijira domin kauce wa hukuncin dauri kan almundahana da aka yanke masa a shekarar 2008.

’Yan uwan biyu suna da farin jini a wurin talakawan kasar Thailand, amma ’yan boko a birane da alkaryu suna adawa da su. 

Zai yi wahala ta yi zaman kurkuku, kasancewar ba ta kasar. An dauki shekara biyu ana gudanar da wannan shari’a inda aka sa ran yanke hukunci a karshen wata Agusta, inda Misis Yingluck ta gaza bayyana a gaban kotu, lamarin da ya tilasta aka dage yanke hukuncin tare da bayar da umarnin a kamo ta.