An yanke wa uba hukuncin daurin shekara biyu saboda bude wasikar dansa
Kotu ta yanke wa wani mutumin kasar Sifaniya hukuncin dauri a gidan yari na shekara biyu, saboda bude wasikar da aka rubuta da adireshin dansa mai shekara 10, wanda aka yi amfani da ita wajen shaidar shari’ar da ake yi wa mahaifiyar yaron. A zaman sauraren shari’ar a kotun Sebille da ke birnin Sifaniya, ana […]
Kotu ta yanke wa wani mutumin kasar Sifaniya hukuncin dauri a gidan yari na shekara biyu, saboda bude wasikar da aka rubuta da adireshin dansa mai shekara 10, wanda aka yi amfani da ita wajen shaidar shari’ar da ake yi wa mahaifiyar yaron.
A zaman sauraren shari’ar a kotun Sebille da ke birnin Sifaniya, ana tuhumar mahaifin yaron akan laifin yi wa dansa binciken wasika da ta ke dauke da adireshin sunan dan wanda hakan ya sabawa doka.
An dai tura wasikar ne ta hanyar kanwar mahaifiyar yaron, an bayyana yadda zai zama shaida game da tuhumar da ake yi wa mahaifin yaron na laifin cin mutuncin mahaifiyar yaron da ya yi a shekarar 2012.
Kanwar mahaifiyar yaron ta bayar da rahoton cewa, wasikar na bayyana cin mutuncin mahaifiin yaron, wanda aka shirya amfani da ita a kotu don tabbatarwa kotun yaron ya zama shaida game da cin mutuncin da mahaifinsa ya yi wa mahaifiyarsa.
Sai dai mutumin bai amince da laifin da ake tuhumarsa da shi ba, amma a yanzu yanke masa hukuncin dauin shekara biyu da kuma biyan tarar kudi saboda karya dokar binciken sirrin wani.
Mahaifiyar yaron ce ta shigar da karar don daukan mataki game da tsohon mijinta bisa tuhumarsa da karanta bayanan sirri. Ta hanyar amfani da alkalinta inda tsohuwar matar ta bukaci a yankewa tsohon mijin hukuncin daurin shekara biyu da biyan tarar kudi Dalar Amurka $3,340 dai da Naira miliyan 1, dubu 23 da dari 5 da 43 (1,023,543). Kamar yadda majiyar kafar sadarwa La Banguardia ta sanar, kuma alkalin ya bukaci biyan karin kudi 6 euro daidai da Naira dubu 2061.89 a kowace rana na tsawon wata 12, jumullar adadin kudin ya kai euro 2,160 daidai da Naira 742,280.62
Mahaifin yaron ya ce ya bude wasikar bisa kuskure, a cewar lauyansa ya ce mahaifi ya na iya amfani da ’yancinsa na mahaifi wajen binciken abin dan sa.
Lauyan da ke kare wanda aka kai kara ya bukaci kotun ta dubi wannan damar da mahaifi ke da shi game da ikon da yake da shi akan dansa. A yanzu haka alkalin ya na shirin yanke hukunci na karshe.